Zaben 2019: Manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Zaben 2019: Manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

- Sama da mambobin jam'iyyun siyasa 173 da suka hada da PDP, SDP, ADC da sauransu, zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a Adamawa

- Wadanda suka sauya shekar sun yi hakan ne la'akari da namijin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayar da aikin titin Mayobelwa zuwa Toungo

- Taron yakin zaben a cewar wani da ya ganewa idanuwansa, ya ce ya linka taron da APC ta yi na 2015 sau 10 kuma akwai kamshin nasara a zaben jihar mai zuwa

Sama da mambobin jam'iyyun siyasa 173 ne suka sauya sheka daga jam'iyyun nasu da suka hada da PDP, SDP, ADC da sauransu, zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, a karamar hukumar Toungo da ke cikin jihar Adamawa.

Wadanda suka sauya shekar, sun bayyana cewa sun yanke wannan shawarar ne ta komawa APC saboda irin ayyukan raya kasa da al'umma da gwamnan jihar, Mohammed Jibrilla Mohammed ya aiwatar.

Tare da kuma yin la'akari da namijin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayar da aikin titin Mayobelwa zuwa Toungo, wanda ya sa suka kuma sha alwashin kad'a masa kuri'unsu a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Ana wata ga wata: APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin yakin zabe

Zaben 2019: Manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Zaben 2019: Manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa
Source: Twitter

Babban daraktan yakin zaben Bindo Chief Felix Tangwami ya shaidawa dubunnan magoya bayan APC a garin Jada, Ganye da kuma Toungo cewa gwamnan jihar, Bindo, na a shirye domin yin aiki tukuru wajen ganin jihar Adamawa ta ci gaba da al'ummar da ke cikinta.

"Mun zo yau ne domin jaddada maku cewa duk wani alkawari da Bindo ya dauka, to kuwa zai cika shi. Ina baku tabbacin cewa za a gudanar maku da ayyuka a Toungo, kamar yadda kuka gani a baya haka zaku gani a gaba. Ku dai ku fito ku zabi Buhari da Bindo," a cewarsa.

Wannan taron, a cewar wani da ya ganewa idanuwansa, ya ce ya linka taron da APC ta yi na 2015 sau 10 kuma akwai kamshin nasara a zaben jihar mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel