‘Yan siyasa na neman kawo hatsaniya a zaben 2019 – inji NSA Munguno

‘Yan siyasa na neman kawo hatsaniya a zaben 2019 – inji NSA Munguno

Mun ji cewa Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a game da harkokin tsaro watau Babagana Monguno, ya bayyana cewa wasu manyan ‘yan siyasa na neman kawo hargitsi a zaben 2019.

‘Yan siyasa na neman kawo hatsaniya a zaben 2019 – inji NSA Munguno

Akwai ‘Yan siyasan da ke yunkurin tada rikici a zaben bana
Source: Facebook

Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ya bayyana cewa ‘yan siyasan da ke tsoron faduwa zaben bana su na kokarin shirya yadda za a tada rikici da tarzoma a zaben. Janar Munguno yace gwamnati ba za ta yarda da wannan ba.

NSA Babagana Monguno yayi wannan jawabi ne wajen wani taro da jami’an tsaro su kayi da gwamnonin Najeriya a babban birnin tarayya Abuja. An yi wannan taro ne jiya Talata inda gwamnonin jihohin kasar duk su ka halarta.

Munguno yace jami’an tsaro sun shirya tsaf domin takawa duk wani mai kokarin jefa kasar nan cikin wani hali na rikici. Mai ba shugaban kasar shawara yace ba za su bari a rika amfani da ‘yan daba ko a rika yawo da makamai tsirara ba.

KU KARANTA: Magoya bayan PDP 2,500 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina

NSA din yake cewa ya samu labari cewa wasu na kutun-kutun din hargitsa kasar nan a daidai lokacin zabe saboda sun hango za su sha kasa inda yayi alkawarin tashi tsaye wajen hukunta duk masu irin wannan mugun nufi a Najeriya.

Ofishin na ONSA na mai ba shugaba Buhari shawara a kan sha’anin tsaro sun gama shiri na tsare rayukan jama’a. Babagana Munguno ya fadawa gwamnonin kasar cewa zai hada kai da sauran hukuma wajen ganin an yi zaben 2019 lafiya.

Jiya mu ka ji cewa Bola Tinubu yayi wa Atiku Abubakar raddi a game dakatar da CJN yana mai cewa Onnoghen yana iya komawa kan kujerar sa nan gaba kamar yadda PDP ta cigaba da kamfe bayan ta dakatar da yakin zaben na wani lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel