Tinubu ya kare Buhari yayi wa Atiku raddi a kan rikicin dakatar da babban Alkalin Najeriya

Tinubu ya kare Buhari yayi wa Atiku raddi a kan rikicin dakatar da babban Alkalin Najeriya

Bola Tinubu wanda jigo ne a jam’iyyar APC yayi magana a kan ce-ce-ku-cen da ake tayi na dakatar da Walter Onnoghen daga kan kujerar Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Tinubu ya kare Buhari yayi wa Atiku raddi a kan rikicin dakatar da babban Alkalin Najeriya

Tinubu yace akwai yiwuwar Onnoghen ya koma kan kujerar sa
Source: Twitter

Bola Tinubu yayi jawabi ne yana mai maidawa Atiku Abubakar mai neman takarar shugaban kasa a PDP martani. Atiku ya zargi babban abokin gaban siyasar na sa na 2019 watau shugaba Buhari da yi wa bangaren shari’a karfa-karfa.

Tinubu ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike game da zargin da ke kan wutan Walter Onnoghen, kuma aka same sa ba tare da laifi ba, babu makawa zai koma kan kujerar sa, domin kuwa dama can ba tsige sa aka yi ba.

KU KARANTA: NJC za tayi hukunci a kan Onnoghen da sabon CJN Tanko

Asiwaju Bola Tinubu yace shugaban kasa Buhari ya dakatar da Onnoghen ne saboda a gudanar da shari’ar sa ba tare da jin tsoro ko kokarin yi wa shari’a katsalandan. Ana zargin Onnoghen ne da yin karya wajen bayyana kadarorin sa.

Jigon na APC ya zargi Atiku da yi wa Duniya karya da kuma murde gaskiya a jawabin da yayi kwanaki yana mai sukar matakin da shugaban kasa Buhari ya dauka na nada sabon Alkalin Alkalai ba tare da samun goyon bayan shari’a ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya soki Atiku na ikirarin da yayi na cewa ya dade yana gwagwarmaya saboda damukaradiyyar Najeriya. Tinubu yace idan har gaskiya ne Atiku ba zai nemi yayi takarar shugaban kasa tsofai-tsofai da shi ba.

Bola Tinubu yace Atiku ya fara hangen kujerar Buhari ne sai yanzu da ya ga abubuwa na neman cabe masa yake kukan cewa an yi wa tsarin mulki karon-tsaye, alhali kuwa sam ba haka abin yake ba, sai dai ana zargin Onnoghen din ne da laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel