Kai-ya-rabu: An samu sabani tsakanin Shugaba Buhari da shugaban APC, Oshiomhole

Kai-ya-rabu: An samu sabani tsakanin Shugaba Buhari da shugaban APC, Oshiomhole

An samu wata 'yar karamar dirama ranar Talata da ta gabata a garin Owerri na jihar Imo wajen zabayen gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari.

Mun samu cewa dai kawuna sun rabu ne biyo bayan sabanin da aka samu saboda rikicin da yanzu haka ke tsakanin uwar jam'iyyar ta APC a mataki na tarayya karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole da kuma gwamnan jihar, Cif Rochas Okorocha.

Kai-ya-rabu: An samu sabani tsakanin Shugaba Buhari da shugaban APC, Oshiomhole

Kai-ya-rabu: An samu sabani tsakanin Shugaba Buhari da shugaban APC, Oshiomhole
Source: Facebook

KU KARANTA: Fitattun yan Najeriya 2 sun tsagewa Buhari gaskiya

Legit.ng Hausa ta fahimci rashin hadin kai a tsakanin jiga-jigan 'yan APC a jihar ne dai lokacin da Shugaba Buhari ya fadawa 'yan jihar cewa su zabi wanda ran su ya kwantamawa ba sai lallai dan jam'iyyar sa ta APC ba sabanin yadda yake fada a sauran jahohi.

Wannan dai kamar yadda muka samu, ya zo ne dai jim kadan bayan Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Oshiomhole yayi kira da a zabi dan takarar gwamna a APC na jihar yayin da kuma shi gwamnan jihar yace ba zai goya masa baya ba.

Mai karatu dai zai iya cewa jami'iyyar Action Alliance (AA) wadda ta tsaida Mista Uche Nwoso da kuma ke da goyon bayan gwamnan jihar sun ce za su goyi bayan shugaban kasa yayin da su kuma jam'iyyar APC suka tsaida Senata Hope Uzodinma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel