An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mata 13 daga Zamfara

An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mata 13 daga Zamfara

A iya cewa har yanzu jahar Zamfara bata rabu da matsalar tsaro ba duk da irin rahotannin da ake samu dake nuna nasarorin da dakarun Sojin Najeriya ke samu a kokarinsu na kakkabe jahar daga ayyukan yan bindiga, da ma sauran jihohin dake makwabtaka da ita.

Anan ma wasu gungun yan bindiga ne suka yi awon gaba da mata guda goma sha uku a wani harin gida gida da suka kai kauyen Majema dake cikin karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, inji rahoton jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: Na cika alkawarin dana dauka a shekarar 2015 – Buhari ga yan Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne daren litinin, 28 ga watan Janairu, kimanin kwana guda kenan bayan wasu yan bindiga sun kai hari a wani gidan kallon kwallo, inda suka tafi da mutane bakwai a karamar hukumar Birnin Magaji.

Wani mazaunin garin Majema ya shaida ma majiyarmu cewa da misalin karfe 11:30 na daren litinin yan bindigan suka kutsa kai cikin garin, inda suka fara harbin mai kan uwa da wabi da nufin razana mazauna kauyen.

“Daga nan suka fara bin gida gida suna tattaro mutane, suna tarasu a karkashin wata babbar bishiyar mangwaro dake wajen garinmu, sun shiga akalla gidaje bakwai a yayin da suke bin gida gida, sun sake kama wata mata da suka bukaci ta nuna musu gidajen masu kudin garin, amma ta ki.

“Nan take suka buga mata kan bindiga, ta fadi sumamma akan titi, a haka suka rabu da ita, bayan sun gama tattara mutanen ne suka tasa keyarsu zuwa cikin daji.” Inji shi.

Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar Zamfara, SP Mohammad Shehu ya bayyana cewa jami’an Yansanda sun samu nasarar fatattakar yan bindigan daga kauyen, inda yace tare da Sojoji da matasan JTF suka fatattakesu.

“Sakamakon harin da muka kaddamar musu yasa yan bindigan suka tsere zuwa dajin dumburum, sai daga bisani a yayin da muke tattara bayanai muka gano ashe tuni sun yi awon gaba da mutane 13.” Inji shi.

Daga karshe Mukhtar ya bada tabbacin rundunar Yansanda na yin iya bakin kokarinta don ganin ta ceto dukkanin mutanen da yan bindigan suka yi garkuwa dasu, amma ya bukaci jama’a dasu taimaka musu da bayanan sirri game da duk abinda suka sani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel