Sai yanzu muka san takamaimen adadin gangan danyen mai da muke fitarwa – Ministan Buhari

Sai yanzu muka san takamaimen adadin gangan danyen mai da muke fitarwa – Ministan Buhari

Yan Najeriya sun dade a cikin duhu anai musu karairayi game da tarin arzikin mai dake zube a cikin kasarsu, amma a karo na farko, gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta gano gaskiyan adadin gangan danyen man da ake fitarwa daga kasar, inji karamin ministan albarkatun man fetir, Ibe Kachikwu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Minista Kachikwu ya bayyana haka ne a ranar Talata, 29 ga watan Janairu a yayin da yake jawabi a taron kara ma juna sani na kwararru a masana’antar man fetir daya gudana a garin Abuja.

KU KARANTA: Na cika alkawarin dana dauka a shekarar 2015 – Buhari ga yan Najeriya

A jawabinsa, Ministan yace a yanzu haka gwamnati na kokarin hada kai da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, wajen bin sawun manyan jiragen ruwa dake dakon danyen mai daga Najeriya zuwa kasashen duniya.

Kachikwu yace sun fahimci akwai badakala a yadda ake safarar wasu daga cikin manyan jiragen dake dakon mai daga Najeriya zuwa sauran sassan duniya, wannan ne dalilin da yasa gwamnati ta hada kai da EFCC don magance matsalar.

Haka zalika ministan yace sabon tsarin bin sawun jiragen dakon mai zai kai ga jiragen dake shigo dsa man fetir Najeriya ta yadda ba tare da an sha wahala ba za’a san adadin fetir da kowanni jirgin dako ya dauke dashi, inda aka ajiyesu, har zuwa lokacin da za’a sayar ma jama’a.

“A karo na farko mun san abinda muke samarwa a kasarnan, kuma mun san lokacin da ake fitar da danyen man, mun san jiragen dake shigowa da fetir Najeriya tare da dukkanin bayanansu, a haka mun kama jiragen ruwa suna tsaye tsaye akan hanya don daukan kayan da ba’a umarcesu su dauka ba.

“Don haka muka hada kai da EFCC domin tattara bayanan jiragen dakon ta yadda zamu san su wanene masu jiragen, ina aka aikesu, me ya faru akan hanyarsu, menene nauyin jirgin da sauransu, da wannan zamu san duk abin dake wakana a masana’antar man fetir a Najeriya.” Inji shi.

A zance mafi inganci Najeriya na fitar da gangan danyen mai miliyan biyu da dubu dari biyar da talatin (2.53m) a kowacce rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel