Idan na mutu yanzu, Buhari ne ya kashe ni - Inji wani gwamna a Arewa

Idan na mutu yanzu, Buhari ne ya kashe ni - Inji wani gwamna a Arewa

Gwamnan jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, Samuel Ortom ya bukaci 'yan Najeriya da su dora alhakin dukkan wani abu da ya same shi da iyalan sa akan shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin da yake shugaban ta.

Gwamna Ortom ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a masaukin sa na gidan gwamnatin jihar a unguwar Asokoro, garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda yayi ikirarin cewa yanzu gwamnatin tarayya ta taso shi gaba.

Idan na mutum yanzu, Buhari ne ya kashe ni - Inji wanin gwamna a Arewa

Idan na mutum yanzu, Buhari ne ya kashe ni - Inji wanin gwamna a Arewa
Source: UGC

KU KARANTA: Sojoji da farar hula da dama sun bace bayan harin 'yan Boko Haram

Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan na Benue ya kara da cewa yanzu hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawa sun koma karnukan farautar gwamnati ne kawai dake yakar 'yan adawa.

Ya cigaba da cewa tun da ya koma jam'iyyar PDP yake fuskantar matsala da matsin lamba tare da bincike kala-kala wani lokacin ma hadda barazana daga jami'an gwamnatin duk kuwa da irin kokarin da yake yi wa jama'ar sa.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan an ce yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kaca-kaca akan dakatar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen da yaya a satin da ya gabata tare kuma da bashi shawarar cewa yabi mulki ahankali.

Goodluck Jonathan kamar yadda muka samu, ya shawarci shugaba Buhari da ya dena bari giyar mulki na daukar sa wajen muzgunawa abokan hamayyar sa da karfin da yake da shi a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel