Wasu fitattun 'yan Najeriya 2 sun kwancewa Buhari zani a kasuwa

Wasu fitattun 'yan Najeriya 2 sun kwancewa Buhari zani a kasuwa

Wasu fitattun 'yan Najeriya da suka hada da tsohon Sakataren dindin din na majalisar dinkin duniya Cif Emeka Anyaoku da kuma shugaban darikar Katolika ta shiyyar Sokoto Bishop Matthew Kukah sun fadawa Shugaba Buhari gaskiya game da salon mulkin sa.

Da suke gabatar da jawaban su a lokutta daban-daban a wajen bikin cikar jaridar Nigerian Tribune shekaru 70 da kafuwa, fitattun mutanen sun ce maganar gaskiya abubuwa da dama ba su tafiya yadda ya kamata a kasar karkashin jagorancin shugaban kasar.

Wasu fitattun 'yan Najeriya 2 sun kwancewa Buhari zani a kasuwa

Wasu fitattun 'yan Najeriya 2 sun kwancewa Buhari zani a kasuwa
Source: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun kubutar da mutane daga 'yan Boko Haram

Legit.ng Hausa ta tsinkayi Cif Emeka Anyaoku na cewa harkokin kasar na cigaba ne da tabarbarewa sakamakon kin sake fasalin kasar da gwamnatin ta shugaba Buhari ta ki yi duk kuwa da irin tarin anfanin yin hakan.

A nashi bangaren, Bishop Kukah cewa yayi a halin yanzu kasar na fuskantar barzana ne musamman a bangaren shari'a inda bangaren zartaswa ke kokarin yiwa kutse da katsalandan.

Ya kara da cewa kusan kowa a Najeriya ya aminta da cewa laifi ne babba Alkalin alkalai ya aikata na kin bayyana kadarorin sa da yayi amma kuma hanyar da aka bi aka cire shi ba daidai bane kuma.

A wani labarin kuma An samu wata 'yar karamar dirama ranar Talata da ta gabata a garin Owerri na jihar Imo wajen zabayen gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari.

Mun samu cewa dai kawuna sun rabu ne biyo bayan sabanin da aka samu saboda rikicin da yanzu haka ke tsakanin uwar jam'iyyar ta APC a mataki na tarayya karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole da kuma gwamnan jihar, Cif Rochas Okorocha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel