PDP ta yi wa Buhari dariya kan taro marar armashi a wata jihar kudancin Najeriya (Hotuna)

PDP ta yi wa Buhari dariya kan taro marar armashi a wata jihar kudancin Najeriya (Hotuna)

Jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) yi ba'a tare da dariya ga shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar su ta All Progressives Congress (APC) kan taron gangamin da suka gudanar a garin Owerri, jihar Imo.

Jam'iyyar ta PDP, wadda ta bayyana taron a matsayin marar armashi da ya tattaro tsirarun mutanen da gwamnati ta siya ta ce hakan yana kara tabbatar wa da al'ummar kasa cewa wa'adin mulkin shugaban kasar fa yazo karshe.

PDP ta yi wa Buhari dariya kan taro marar armashi a wata jihar kudancin Najeriya (Hotuna)

PDP ta yi wa Buhari dariya kan taro marar armashi a wata jihar kudancin Najeriya (Hotuna)
Source: Facebook

KU KARANTA: Jonathan yayiwa Buhari kaca-kaca kan Onnoghen

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na jam'iyyar ta PDP Kola Ologondiyan ya fitar sannan ya rabawa manema labarai.

Haka zalika Mista Kola Ologondiyan ya shawarci yan kasar da su yiwa kansu karatun ta-natsu su kawai da mulkin shugaba Buhari musamman idan akayi duba da irin yadda farin jinin sa ke kara dusashewa.

A wani labarin kuma, A yayin da 'yan kwanaki kalilan suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa, a yau Talata cikin jihar Imo, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci al'ummar Najeriya dangane da 'yan takara da suka cancanci a kada ma su kuri'u a zaben bana.

A yau Talata yayin taron sa na yakin neman zabe, baya ga ra'ayi da kuma akida, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi al'ummar jihar Imo kan zaben 'yan takara da suka cancanta ta fuskar riko da akalar jagoranci.

Ga dai wani hoton nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel