Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa

Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa

- Shitu Kabir, Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APDA yace shugaba Buhari bai yi kuskure ba na dakatar da Onnoghen

- Shugaban yayi hakan ne don kare ra'ayin talakawa

- Amma hakan yasa wasu sun tsorata sakamakon tarwatsa musu shirin su da akayi

Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa

Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa
Source: Depositphotos

Shitu Kabir, Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APDA, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi kuskure ba na dakatar da Walter Onnoghen, alkalin alkalan Najeriya da yayi.

Yace shugaban yayi aiki da ra'ayin talakawa, kari da cewa "Cutar gaggawa na bukatar maganin gaggawa " .

Buhari ya dakatar da Onnoghen ne akan shari'ar da yake fuskanta akan boye kadarorin shi ba tare da ya bayyana ba.

Inda da yawa da suka hada da PDP, sun kushe dakatarwar tare da cewa ta sabawa kundin tsarin mulki, amma fadar shugaban kasan tace abinda ya dace ne ta aikata.

A yayin da yayi magana da manema labarai a Abuja, Kabir yace dakatar da alkalin alkalan "Yayi daidai kuma a lokacin da ya dace".

GA WANNAN: Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

"Da yawan yan Najeriya sun gane hakan yanzu amma saboda matakin da shugaban ya dauka da Onnoghen ya cigaba da hada alkalan zabe," inji shi.

"Ba abin mamaki bane da wasu ke tunanin an tarwatsa musu shirin su."

Ya karyata cewa dakatarwar yunkuri ce ta jam'iyyar mai mulki wajen daidaita bukatar su a zabe mai zuwa.

"Wannna maganar ma ba abin sauraro bace. Laifi dai za a iya kai karar shi ne tare matukar an gano shi. Dakataccen alkalin alkalan dole ne ya tsaya tare da fuskantar shari'a. Nauyin kuma yana kan mai shari'ar ne da ya wanke kanshi kamar yanda kundin tsarin mulki ya tanadar. A lokacin lokacin ne za a gane yana da gaskiya ko akasin hakan."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel