Zabe: Bai kamata a bari APC ta tsayar da 'yan takara a Zamfara ba - Sanatan APC

Zabe: Bai kamata a bari APC ta tsayar da 'yan takara a Zamfara ba - Sanatan APC

A yau Talata ne Sanata mai wakiltan Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Marafa ya sake jadada cewa bai dace a bari jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da 'yan takara ba a zaben da za a gudanar a watan Fabrairu da Maris na wannan shekarar.

Marafa ya ce Hukumar Zabe mai zaman kanta tayi biyaya da umurnin babban kotun Abuja inda ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta fitar da 'yan takara ba.

Sanatan wanda kuma shine Ciyaman din kwamitin majalisar dattawa a kan albarkatun man fetur ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da menema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya ce INEC ta tsaya a kan bakar ta na haramtawa jam'iyyar APC reshen Zamfara fitar da 'yan takara saboda gaza gudanar da zaben fidda gwani a cikin lokacin da aka kayyade mata.

Zabe: Bai kamata a bari APC ta tsayar da 'yan takara a Zamfara ba - Sanatan APC

Zabe: Bai kamata a bari APC ta tsayar da 'yan takara a Zamfara ba - Sanatan APC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Marafa wadda dan jam'iyyar APC ne ya ce barin APC ta shiga zaben na 'yan majalisar tarayya da gwamnoni zai zama babban zaluncin kuma bai dace a bari hakan ya faru ba.

Marafa ya ce: "Ni cikaken dan jam'iyya ne kuma ina biyaya ga jam'iyya sai dai biyayar ba na rufa ido bane musamman lokutan da ake bukatar adalci.

"Biyaya ta na farko ga kasa ta Najeriya ce saboda idan babu Najeriya, ba zamu samu Majalisar Tarayya ba balantana mu samu jam'iyyun siyasa.

"Saboda haka, biyaya ta na farko ga Allah ne sai kuma al'umma ta. APC ba addini bane. Saboda haka idan APC suka ce dan takara mafi muni a APC yafi dan takarar da ke da nagarta a wata jam'iyyar, zan biye musu saboda siyasa ce kuma suna son su lashe zabe ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel