Harkallar Alkalin-Alkalai: Jonathan yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Harkallar Alkalin-Alkalai: Jonathan yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan an ce yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kaca-kaca akan dakatar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen da yaya a satin da ya gabata tare kuma da bashi shawarar cewa yabi mulki ahankali.

Goodluck Jonathan kamar yadda muka samu, ya shawarci shugaba Buhari da ya dena bari giyar mulki na daukar sa wajen muzgunawa abokan hamayyar sa da karfin da yake da shi a yanzu.

Harkallar Alkalin-Alkalai: Jonathan yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Harkallar Alkalin-Alkalai: Jonathan yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Mumbalin kamfe ya rufta da dan takarar gwamna a PDP

Legit.ng Hausa ta samu cewa tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a garin sa na Bayelsa yayin da yake jawabi a wajen cigaba da taron gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Haka zalika Goodluck Jonathan ya gayawa shugaban kasar cewa sahihin zabe ne kawai a ranar 16 ga watan Fabreru zai sa kasar Najeriya ta zauna lafiya kuma a cigaba da zama kasa daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel