Buhari ya kaddamar da wani katafaren aikin wutar lantarki a Jihar Abia

Buhari ya kaddamar da wani katafaren aikin wutar lantarki a Jihar Abia

- Buhari ya kai wuta cikin kasuwan Ariaria a Jihar Abia

- Shugaban kasar yace lantarki ba ta da Jam’iyyar siyasa

- Dazu fadar Shugaban kasar ta fitar da wannan jawabi

Buhari ya kaddamar da wani katafaren aikin wutar lantarki a Jihar Abia

Wutar lantarki ba ta da Jam’iyyar siyasa inji Shugaba Buhari
Source: Facebook

Dazu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani katafaren aikin wutar lantarki da aka yi a jihar Abia da ke cikin yankin Kudancin Najeriya. Shugaban kasar yace wannan kadan ma aka gani daga cikin aikin gwamnatin sa.

A yau Talata ne Buhari ya bude aikin wutan lantarki da aka zuba a kasuwar garin Ariara da ke jihar Abia inda shaguna akalla 37000 za su amfana. Wannan yana cikin kokarin gwamnatin tarayya na kawo ayyukan da za su taimakawa jama’a.

KU KARANTA: Ko a jiki na: Ba zan ji haushi don APC ta sha kasa ba - Sanatan Zamfara

Shugaban kasar ya bayyana cewa idan aka zo maganar duhu da haske, babu ruwan lantarki da banbancin akidar siyasa. Jawo wutan lantarkin da aka yi zuwa kasuwar ta Ariara za ta taimaka kwarai wajen samun wutan yin aiki a shago.

Buhari yace gwamnatin sa za ta cigaba da kokarin ganin ta kawo ayyukan da za su taba rayukan al’umma ba tare da kallon akidar siyasa ba. Wannan ya sa gwamnati ta jawo wuta saboda kasuwancin mutanen Abia ya bunkasa da kyau.

‘Yan kasuwar na Abia su kan kai kayan su a saya har zuwa kasashen kusa irin su Chad, Kamaru, Gambia da kasar CAR. Kafin yanzu dai ba a samun wutan lantarki a kasuwar sai yanzu da Buhari ya kawo dauki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel