Atiku ya kai kara US, UK, EU, ya lissafo zunuban Buhari

Atiku ya kai kara US, UK, EU, ya lissafo zunuban Buhari

- Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya rubuta wasika ga kasashen Amurka, Ingila da Tarayyar Turai

- Tsohon shugaban kasar ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin barazana ga damokradiyyar Najeriya

- Atiku ya lissafa zunuban shugaban kasar daya bayan daya

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya rubuta wasika ga kasashen Amurka, Ingila da Tarayyar Turai, inda yayi zargin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a barazana ga damokradiyyar Najeriya.

Atiku, a wasikar mai kwanan wata 27 ga watan Janairu, 2019, zuwa ga jakadan Amurka, Ingila da Tarayyar Turai a Najeriya ya zargi Buhari da karya dokar kundin tsarin mulin kasa da kuma rusa hukumomin kasar.

Atiku ya kai kara US, UK, EU, ya lissafo zunuban Buhari

Atiku ya kai kara US, UK, EU, ya lissafo zunuban Buhari
Source: Twitter

A wasikar, Atiku ya nemi gwamnatocin wadannan kasashe da su matsawa gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) da ta janye daga zargin take hakki da kuma tabbatar da cewar an bayar da filin daga ga dukkanin yan takara a zabe mai zuwa.

“Ina rubuta wannan wasika a matsayina na mai aiki tare da kasashen duniya don ganin ci gaban Najeriya da kuma karfafa damokradiyarmu da kuma kawo sauyi ga tattalin arzikin kasarmu.

“Yayinda Shugaban asar yayi rantsuwar kre kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, zancen gaskiya shine ya saba rantsuwarsa t hanyar bangaranci da take doka.” Inji Atiku.

KU KARANTA KUMA: Cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya kuma lissafa zunuban Buhari kamar “dakatar da Shugaban alkalan Najeriya Onnoghen, siyan jiragen yaki ba bisa ka’ida ba, rashin bin umurnin kotu da kamar kin sakin Ibraheem El-Zakzaky Shugaban kungiyar Shi’a akan beli, da Kanal Sambo Dasuki, tsohon mai ba kasa shawara a harkokin tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel