Dakatar da CJN: Matasan Arewa sun goyi bayan Buhari

Dakatar da CJN: Matasan Arewa sun goyi bayan Buhari

- Matasan Arewa sun gudanar da zanga-zangan nuna goyon bayansu ga Shugaba Buhari a kan dakatar da Walter Onnoghen

- Matasan sun bayyana cewa wadanda ke neman a mayar da Onnoghen kan mukaminsa makiyan Najeriya ne

- Matasan sun bukaci ayi gaggawar sallamarsa tare da gurfanar da shi a gaban kuliya domin ya fuskanci hukunci laifin da ya aikata

Wata hadakar kungiyoyin arewa a jihar Kaduna sun bayyana goyon bayansu a kan matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen inda har suka bukaci ya yi murabus daga mukaminsa.

Matasan sun fita sunyi zanga-zanga a tituna inda suke nuna rashin amincewarsu da wadanda ke nema a mayar da Alkalin Alkalan a kan mukaminsa.

Dakatar da CJN: Matasan Arewa sun goyi bayan Buhari

Dakatar da CJN: Matasan Arewa sun goyi bayan Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Masu zanga-zangan sun zaga manyan titunan jihar Kaduna dauke da alluna da takardu masu dauke da sakonni da ke yabawa Shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarin da ya ke yi na kawar da rashawa a fannin shari'a kuma suke shawartarsa ya cigaba da dagewa.

A yayin da suke magana da manema labarai, shugabanin kungiyoyin sun ce wadanda ke neman a mayar da Alkalin Alkalan makiyar Najeriya ne, sun kuma gargadi mutane da ke kokarin danganta tsige Onnoghen da kabilanci ko addini.

A cewarsu, Justice Onnoghen ya saba doka ta hanyar kin bayyana wasu kadarorinsa ga Kotun Da'ar Ma'aikata saboda haka ya dace ya yi murabus ne a maimakon ya rika kaiwa da komowa a kotu.

Matasan sun ce dakatar da CJN shine mataki na farko kuma suka bukaci ayi gaggawar sallamarsa tare da gurfanar da shi a kotu ya domin ya gurbi abinda ya shuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel