Bayan Dogara, wasu 'yan majalisa biyu sun sake komawa PDP

Bayan Dogara, wasu 'yan majalisa biyu sun sake komawa PDP

Kakakin Majalisar Dattawa, Yakubu Dogara ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa babban jam'iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP).

Kakakin Majalisar ya bayar da sanarwar ne a fadar Majalisar a zaman da akayi a yau Talata.

Har ila yau, Kakakin Majalisar ya sanar da ficewar wasu 'yan majalisar biyu zuwa jam'iyyar ta PDP, Edward Pwajok da Ahmed Yerima.

Tun a watan Satumban 2018 ne dai Kakakin Majalisar ya nuna alamar cewa zai fice daga jam'iyyar ta APC a lokacin da ya ziyarci sakatariyar PDP na kasa da ke Abuja ya mika fam din takarar Majalisar na Wakilai.

Bayan Dogara, wasu 'yan majalisa biyu sun sake komawa PDP

Bayan Dogara, wasu 'yan majalisa biyu sun sake komawa PDP
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Ya dauki wannan matakin ne bayan daruruwan magoya bayansa daga mazabun Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi zun ziyarci shi inda suka gabatar masa da fam din takara na PDP kuma suka bukaci ya fice daga APC.

Tun da dadewa, mutane suna kyautata zaton Dogara zai fice daga jam'iyyar ta APC saboda irin sa in sa da suke yi da Gwamna Mohammed Abubakar na jihar ta Bauchi.

Akasin yadda sauran 'yan majalisar suka sanar da sauya shekarsu tun a baya, Dogara bai bayyana nasa ba har sai da aka zo zama na karshe kafin babban zaben 2019.

A yayin da ya ke jawabi a ofishin PDP, Dogara ya ce ya fice daga jam'iyyar APC.

"Na yanke shawarar dawowa," Dogara ya fadawa dimbin magoya bayansa da ke cike da murna a yayin da ya ke mayar da fam din takarar 2019.

Ya ce jam'iyyar APC bata cika alkawurran da ta dauka a jihar Bauchi ba hakan yasa ya fice daga jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel