Atiku zai iya kawo hadin kai a kasa - Jonathan

Atiku zai iya kawo hadin kai a kasa - Jonathan

- Tsohon Shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan yace dan takarar Shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar zai iya kawo hadin kai a kasar

- Jonathan yace Atiku na kaunar mutanen Bayelsa sannan ya bukaci da su zabe shi

- Atiku ya jadadda alkawarinsa na tallafawa mata da matasa idan har yayi nasara a zabe

Tsohon Shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan yace dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar mutum ne da zai iya kawo hadin kai da wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Jonathan yayi magana a ranar Talata, 29 ga watan Janairu a Ox-bow Lake Pavillion da ke Yenagoa, lokacin da jirgin kamfen din Atiku ya isa jihar Bayelsa.

Atiku na da karfin iya hada kan kasa - Jonathan

Atiku na da karfin iya hada kan kasa - Jonathan
Source: Twitter

Tsohon Shugaban kasar yace Atiku na kaunar mutanen Bayelsa sannan ya bukaci da su zabe shi.

Ya bukaci yan siyasa da su daina amfani da kujerar mulki suna muzgunawa mutane.

“Kada kujerar siyasa ya zama abun amfani wajen muzgunawa mutane.

“Atiku na kaunar mutanen jihr Bayelsa da Ijaw sannan ya fahimce su sosai."

A wajen gangamin, Atiku ya jadadda alkawarinsa na tallafawa mata da matasa idan har yayi nasara a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

A wani lamari na daban, mun ji cewa wani bangare na kungiyar Yarbawa na Afenifere sun amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo a matsayin yan takararsu na Shugaban kasa a zaben za a gudanar a watan gobe.

Hakan na zuwa yan kwanaki bayan kungiyar yan Igbo ta Ohaneze Ndigbo ta tsayar da Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda za ta marawa baya a zaben Shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel