2019: Ina goyon bayan kudirin tazarcen Gwamna Ganduje - Mahaifin Kwankwaso

2019: Ina goyon bayan kudirin tazarcen Gwamna Ganduje - Mahaifin Kwankwaso

Mun samu cewa, Mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, kuma Dagacin garin Madobi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, ya bayyana goyon bayan sa kan kudirin neman tazarce na gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, kuma Dagacin garin Madobi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, ya ara ya kuma ya yafa akidar goyon bayan kudirin neman tazarcen gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Sanatan Kano ta Tsakiya; Rabi'u Musa Kwankwaso

Sanatan Kano ta Tsakiya; Rabi'u Musa Kwankwaso
Source: Depositphotos

Tsohon da ya kasance Mahaifi ga Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya, ya ce zai yi aiki tukuru tare da ribatar rawanin sa wajen hadin kan dukkanin sarakunan gargajiya da ke karkashin karamar hukumar Madobi wajen tabbatar da nasarar Gwamna Ganduje a yayin babban zabe da za a gudanar a watan jibi.

Domin ramawa Kura kyakkyawar aniyarta, Alhaji Saleh ya ce goyon bayan Gwamna Ganduje na da tasirin gaske a sakamakon kwazo da kuma bajintar sa akan kujerar mulki da ta tabbatar da ci gaba da inganta jin dadin al'umma a dukkanin lunguna da sako da ke fadin jihar.

Yayin yabawa kwazon gwamnatin Ganduje, Alhaji Saleh ya ce za su ci gaba da goyon bayan sa tukuru domin al'ummar Kano su yalwata wajen sharbar romon dimokuradiyya da gwamna Ganduje ya riga da saba ma su da ita.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta yi amfani da Mafarauta domin yaki da ta'addanci

Cikin nasa jawaban, Gwamna Ganduje ya ce ya ziyarci garin Madobi domin neman aminci gami da tabarrakin iyaye yayin da ya sa gaban sa tare da hankoron sake maye gurbin kujerar sa a zaben gwamna da za a gudanar a ranar 2 ga watan Maris.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Ganduje ya kuma sha alwashi ga dukkanin Sarakunan gargajiya da kuma Limamai na garin Madobi wajen ninka kwazon sa yayin da ya sake cimma nasara a karo na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel