Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

- Amurka ta fado kar a sabon rahoton, yayin da ita kuma Najeriya tayi sama

- Siyasar Amurka kullum cikin zai take tunda Trump ya dare mulki

- Najeriya na da maki 20 su kuwa Amurka suna da 70 bisa dari

Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu
Source: UGC

A kokarin da Amurka keyi na dawo da martabarta, wanda shugaba Trump yayi wa lakabi da MAGA, watau Make America Great Again, an sami cikas bayan da aka sami karuwar cin hanci a gwamnati a shekarar bara, kamar yadda rahoto ya nuna.

Sai dai a dai-dai lokacin da Amurka ta rasa maki hudu ta dawo taci 71 ne cikin dari, Najeriya har yanzu tana kusa da 20-25, cikin dari, wanda ke nuna duk da haka an fi sata a Najeriya maimakon na sauran kasashe masu ci gaba.

GA WANNAN: Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

Batun cewa wai Najeriya ta rage cin hanci, a cewar masana, wannan ba gaskiya bane, a yadda alkalumman suka nuna tsaye ake cas, sai dai wasu sunfi kasar cin hanci, lamari da yasa suka yo kasa mu kuma muka hau kan kasashe har hudu.

Ita kuwa Amurka, tun 2011 bata sake ganin cin hanci da almundahana irin a wannan lokaci ba. Watau zamanin Obama kenan.

Ko a watan jiya, sai da hukumomi suka tilsastawa shugaba Trump rufe wasu ofisoshinsa na sadaqa, bayan da aka gano hanyoyi ne kawai na sabule wa gwamnati kudadenta da sunan jin qai.

Amurkar ma dai, sai da ta rasa aiki aka ruffe gwamnati tun karshen bara har zuwa wannan makon, saboda wai shugaban naso sai an bashi dala biliyan biyar don yayi bangon kare Amurka daga bakin haure a kudancin kasar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel