An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

- Sojin ruwan Najeriya sun cafke wasu mutane 19 da kayayyakin fetur shakare da kananan jiragen ruwa biyu

- Tuni suka mika su ga hukumar yaki da rashawa don bincike

- An kuma kama su da tsabar kudi har Naira miliyan 3.5

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja
Source: Facebook

Sojojin ruwan Najeriya sun mika mutane 19 da aka kama da kananan jiragen ruwa biyu shakare da kayayyakin man fetur ga hukumar yaki da rashawa don bincike.

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja
Source: Facebook

Wadanda ake zargin da zama barayin fetur sun hada da Ayeni John, Adetini Ademola, Saliu Malik, Emmanuel Tosu, Emopin Moneyin, Malade Aiyetimiyi, Oduroja Ojune, Ikudehinbu Idowu, Abogun Ota, Elamah Augustine da Oalrotimi Elikanah.

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja
Source: Facebook

Sauran sun hada da Thank God Benjamin, Abbas Friday, Victor Goldsmith, Gbenga Thomas da sauran su.

An kamasu ne a ranar 30 ga watan Augusta 2018 a Legas da wani sashi na jihar Ondo kuma ana zargin su ne da mu'amala da kayayyakin fetur ne ba bisa ka'ida ba.

GA WANNAN: OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

An samu wadanda ake zargin da Naira miliyan 3.5 a gurin wadanda ake zargin yayin kama su wanda ake zargin sun samesu ne ta hanyar siyar da kayayyakin man fetur din da suka samu ta haramtacciyar hanya.

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja

An cafko masu satar mai a gabar ruwan kasar nan, an kawo su Abuja
Source: Facebook

Idris Abdullahi Abubakar, mai bincike a hukumar EFCC wanda ya karbi wadanda ake zargi zargin da kananan jiragen ruwan a madadin hukumar, ya tabbatar wa da sojin ruwan cewa za a tsaurara bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya matukar an kammala bincike.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel