Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar

Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar

Dan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya cigaba da yakin neman zabensa a yankin kudu maso kudancin Najeriya inda ya garzaya jihar Bayelsa a yau.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya samu kyakkyawan tarba a jihar kasancewar jihar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne.

Atiku yayi jawabi a taron yakin neman zaben inda ya soki shugaba Buhari da jam'iyyar APC. Yace: "Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi watsi da kundin tsarin mulkin Najeriya. Babban dan kama karya ya zama yanzu. ya shigo a matsayin shugaban kasan farar hula amma an waye gari ya sanya kayan soja."

"Jihar Bayelsa, na zo in gode muku ga soyayyarku ga PDP da Najeriya. Wannan zaben mai zuwa, za'ayi domin rana goben matanmu da matasanmu ne. Kamar yadda kuka sani, domin cigaba da aiki, a zabi PDP."

Shi kuma shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya ce: "Atiku hamshakin dan kasuwa ne. Dukkan kasuwancinsa na nan daram-dam. Jami'arsa ce mafi kyau a Afrika. Shine wanda ya fahimci Najeriya."

Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar

Atiku Abubakar
Source: Facebook

Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar

Magoya bayansa na murna cikin ruwan sama
Source: Facebook

Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar

Hotuna: Yadda mutan jihar Bayelsa suka karbi bakuncin Atiku Abubakar
Source: Facebook

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel