Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye

Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye

- Bincike ya nuna Najeriya na daya daga cikin kasashe masu amfani da kwayoyi ba bisa ka'ida ba

- Akwai karancin wuraren bada shawarwari akan amfani da kwayoyin a kasar

- Yawan aikata laifuka da ta'addancin ya ta'allaka ne da hauhawar mashayan kwayoyi

Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye

Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye
Source: Depositphotos

Tattaunawa da tambayoyi na farko akan amfani da kwayoyi a kasar nan ya nuna cewa mutane miliyan 14.3 masu shekaru 16 zuwa 64 suke amfani da miyagun kwayoyi.

Binciken ya bayyana cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da yawan masu amfani da kwayoyi ba tare da likitoci sun bada dama ba a duniya.

Sakamakon binciken wanda aka saki jiya a Abuja NBS da CRISA tare da tallafin UNODC da EU suka gabatar.

Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye

Kididdiga ta nuna akalla 'yan Najeriya 14m ne ke shaye-shaye
Source: Twitter

Rahoton binciken wanda shine na farko wanda akayi shi a duk fadin kasar nan don gano yawa da yanayin amfani da kwayoyi a Najeriya ya nuna cewa akwai gibi mai girma tsakanin cimma bukatu da kuma kula da mutane masu amfani da kwayoyi.

GA WANNAN: Marafa ya mika godiyarsa ga Zamfarawa bayan da kotu ya bashi tuta

"Da kusan miliyan uku na mutane dake dogaro akan kwayoyi, rashin yawan wuraren bada shawarwari akan amfani da kwayoyi," binciken ya bayyana.

Rahoton wanda aka same shi daga bincika da jin ra'ayoyin mutane 38,850 na gidaje da kuma mutane 9,344 da ke cikin mafi yawan masu amfani da kwayoyi a jihohin fadin kasar nan.

Binciken ya bayyana yawan masu amfani da magungunan tari irin su tramadol da sauran su.

Kamar yanda rahoton ya nuna, hakan ne yasa Najeriya ta zamo cikin kasashe masu amfani da kwayoyi ba bisa umarnin likita ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel