Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna

Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna

- Ana yaki da rashawa tun 2003 a Najeriya

- Har yanzu lamarin kamar karuwa yake

- GA yadda Najeriya taje a Afirka da duniya

Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna

Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna
Source: Facebook

Ana can ana bin diddigin sabon rahoton da kungiyar sanya ido kan cin hanci ta duniya, TI ta fitar, kan bara 2018, na yadda kasashen duniya 180 suka kaya a bara. Najeriya dai ta sami maki 20 cikin dari, in aka bi kadin tarihi da makin da ta samu.

Tun daga mulkin Abacha dai ake daukar alkalumman ake kuma baiwa Najeriya maki, ga kuma yadda abin yake a jere a kowacce shekara.

GA WANNAN: Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

1996: 6.9

1997: 17

1998: 19

1999: 16

2000: 12

2001: 10

2002: 16

2003: 14

2004: 16

2005: 19

2006: 22

2007: 22

2008: 27

2009: 25

2010: 24

2011: 24

2012: 27

2013: 25

2014: 27

2015: 26

2016: 28

2017: 27

2018: 27

Najeriya dai a duniya tazo na 33 a duniya cikin kasashe 180, a Afirka kuwa tazo na 19, inda tazo na 18 a kasashen bakaken fata na Afirka in aka cire larabawan Arewa.

Tsakanin kasashe dai, Najeriya tazo na 148 inda a baya take a 144 a ci gaban kasashe da iya mulki. Sai dai kungiyar ta TI, tace ba wai Najeriya tayi gaba bane, a'a, wasu kasashen ne kawai suka fita barna, don haka suka dawo kasa da ita ita kuma tayi sama ta haure kasashe hudu.

Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna

Duk da yaki da cin hanci da rashawa da aka ce ana yi a Najeriya, ga yadda alkalumman bana suka nuna
Source: Facebook

A karkashin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, gwamnatin Tarayya, ta sanya qaimi sosai kan satar kudin gwamnati, kuma ta kwato biliyoyi daga barayin gwamnati, musamman na wancan zamanin mulkin na PDP.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel