Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta yi amfani da Mafarauta domin yaki da ta'addanci

Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta yi amfani da Mafarauta domin yaki da ta'addanci

- Gwamnatin jihar Borno ta bayyana shirin ta na amfani da Mafarauta domin ci gaba da yakar t a'addanci na Boko Haram

- Gwamna Shettima ya ce gwamnatin sa ta dukufa wajen samar da duk wata bukata ga Mafarauta domin kasancewar su cikin shiri na yaki da ta'addanci

- A cewar gwamnan, samar da ingataccen tsaro ga al'umma na daya daga cikin mafi girman nauyi da rataya a wuyan kowace gwamnati

A jiya Litinin 28 ga watan Janairu, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya yi karin haske kan shirye-shiryen wasu dabaru na gwamnatin sa domin ci gaba da tunkarar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram.

Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta yi amfani da Mafarauta domin yaki da ta'addanci

Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta yi amfani da Mafarauta domin yaki da ta'addanci
Source: Twitter

Gwamna Kashim ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta bullo da wata sabuwar dabara ta ribatar daruruwan Mafarauta domin ci gaba da yakar ta'addancin masu ta'ada da tayar da zaune tsaye a fadin jihar sa.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, gwamnatin Borno a halin yanzu bisa jagorancin dakarun soji ta zage dantsen ta wajen horar da Mafarautan akan barazanar da za su fuskanta a filin daga.

KARANTA KUMA: Ba bu abun da ya shalle ni da faduwar APC a jihar Zamfara - Sanata Marafa

Gwamnan ya yi furucin hakan ne yayin karamci na karbar bakunci da kuma tarairayar sabon Kwamandan Dakarun sojin kasa reshen Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Benson Akinroluyo, da ya ziyarci fadar sa da ke birnin Maiduguri.

Da ya ke jaddada tsayuwar dakan sa wajen dawowa da zaman lafiya da kwaciyar hankali a fadin jihar, Gwamna Kashim ya ce samar da ingataccen tsaro ga al'umma nauyi ne da rataya wuyan kowace gwamnati.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel