Bayan Ohaneze ta tsayar da Atiku, Afenifere ta yanke nata hukuncin

Bayan Ohaneze ta tsayar da Atiku, Afenifere ta yanke nata hukuncin

- Wani bangare na kungiyar Yarbawa na Afenifere sun amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben wata mai zuwa

- Kungiyar ta ce Shugaban kasar ya yi kokari don haka ya cancanci tazarce

- Afenifere ta yaba ma yaki da rashawa da Buhari ya jajirce akai

Wani bangare na kungiyar Yarbawa na Afenifere sun amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo a matsayin yan takararsu na Shugaban kasa a zaben za a gudanar a watan gobe.

Hakan na zuwa yan kwanaki bayan kungiyar yan Igbo ta Ohaneze Ndigbo ta tsayar da Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda za ta marawa baya a zaben Shugaban kasa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa goyon bayan Buhari da Afenifere ta yin a zuwa ne bayan wani ganawa a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo a ranar Talata, 29 ga watan Janairu.

Bayan Ohaneze ta tsayar da Atiku, Afenifere ta yanke nata hukuncin

Bayan Ohaneze ta tsayar da Atiku, Afenifere ta yanke nata hukuncin
Source: Twitter

Kungiyar Yarbawan karkashin jagorancin Ayo Fasanmi tace ta tsayar da Buhari ne saboda ya yi kokari.

A wajen taron harda mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, mataimakan gwamnonin jihohin Lagas da Osun, Fesanmi da Yetunde Onanuga, da kuma wani tsohon minister, Demola Serki wanda ya wakilci tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu.

Wasu daga cikin sarakunan gargajiya da suka hallara sune Ewi na Ado Ekiti, Rufus Adedejuyigbe; Akirun na Ikirun, Abioye Oyebode da Oniye na Iye Ekiti, Adeleye Oni.

KU KARANTA KUMA: Ba saboda kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja

Tsohon sanata, Olabiyi Durojaye ne ya taar da batun tsayar da Buhari da Osinbajon.

Sauran shugabanin Afenifere da suka yoyi bayan lamarin sune Tajudeen Olusi (Lagos), Bayonile Ademodi (Ondo), Yemi Alade (Ekiti), S. M. Akindele (Oyo), da kuma Sooko Adewoyin (Osun).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel