NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan Muhammad da Onnoghen

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan Muhammad da Onnoghen

Hukumar kula da harkokin Shari'a na kasa NJC ta kammala taron gaggawar da ta kira inda ta bawa Alkalin Alkalai Walter Onnoghen da mukadashin Alkalin Alkalai na kasa Tanko Muhmmad kwanaki bakwai domin sun amsa korafe-korafen da aka gabatar a kansu.

A wata sanarwar bayan taro da Direktan yada labarai na NJC, Soji Oye ya fitar, ya ce NJC ta mika korafin da aka shigar a kan Shugaban Kotun Da'ar Ma'aikata CCT, Justice Danladi Umar zuwa ga Umar zuwa ga Hukumar Ayyukan Shari'a na Tarayya (FJSC) wadda ita doka ta bawa daman sauraron irin wannan korafin.

A cewar sanarwar, korafe-korafen da aka shigar a sakatariyar NJC sun hada da:

"Na farko shine korafin da aka shigar a kan Hon. Mr Justice W.S.N. Onnoghen wadda wani Zikhrillahi Ibrahim na Resource Centre for Human Rights and Civil Education ya shigar.

"Na biyu kuma shine korafin da Centre for Justice and Peace Initiative ta shigar a kan mukadashin Alkalin Alkalai na kasa, Ibrahim Tank Muhammad

"Na uku shine korafin da wani Olisa Agabakoba, SAN, OON, ya shigar a kan Hon Justice Ibrahim Tanko Muhammad.

"Na karshe kuma kuma shine korafin da Centre for Justice and Peace Initiative ta shigar a kan Shugaban kotun da'ar ma'aikata CCT, Hon. Danladi Yakubu Umar."

NJC ta mika korafin da akayi a kan Hon. Danladi Yakubu Umar zuwa ga Hukumar Ayyukan Shari'a na Tarayya (FJSC) wadda ita doka ta bawa daman sauraron irin wannan korafin.

Kamar yadda shari'a ta tanada an mika korafin da ake yiwa Justice W.S.N. Onnoghen da I.T. Muhammad a garesu domin su bayar da amsa.

Dubba da irin tuhume-tuhumen da ake musu, hukumar ta rage wa'addin da ake bayarwa na amsa korafi daga kwanaki 14 zuwa kwanaki 7.

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen
Source: Twitter

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen
Source: Twitter

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen

NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan uhammad da Onnoghen
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel