Ba bu abun da ya shalle ni da faduwar APC a jihar Zamfara - Sanata Marafa

Ba bu abun da ya shalle ni da faduwar APC a jihar Zamfara - Sanata Marafa

- Sanatan shiyyar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya ce ba bu ya sha masa kai da rashin dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara na jam'iyyar APC yayin da zaben kasa ke daf da gudana

- Sanata Marafa ya ce gwamnatin Yari na ribatar wasu Sanatoci da tsofaffin gwamnoni wajen ci gaba da rura wutar rikicin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

- Ya kuma ce shugaban kasa Buhari a karan kansa bai da wata damuwa dangane da rashin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar sa ta APC

Dan majalisar dattawa na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, ya ce ba bu abin sha ma sa kai da faduwar jam'iyyar sa yayin zaben kujerar gwamnan jihar da ta kasance ba bu dan takara a halin yanzu.

Sanata Marafa ya ce rashin fidda dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam'iyyar APC ba ya da wani tasiri na damuwa a gare sa da a cewar hakan bai ko kama habar zanin sa ba ballantana kuma ya kai ga jiki.

Sanata Kabiru Marafa

Sanata Kabiru Marafa
Source: Depositphotos

Sakamakon rashin jituwa da tsama ta rabuwar kai a tsakanin jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, ya sanya kawowa yanzu ba bu wani dan takarar gwamna ko kujerar Sanata da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta aminta da shi.

Dan majalisar ya yi zargin yadda gwamnatin Zamfara ke ribatar wasu Sanatoci da kuma tsofaffin gwamnoni na jihar wajen ci gaba da zage dantse na rura wutar rikicin jam'iyyar APC musamman a yankin Arewa maso Yammacin jihar.

KARANTA KUMA: Buhari ya kaddamar da wani babban aiki yayin yakin zaben sa a jihar Abia

Marafa wanda ya zayyana hakan a yau Talata cikin garin Abuja yayin ganawa da manema labarai ya kuma bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a karan kansa ba ya da wani haufi ko damuwa dangane da rashin dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, Sanata Marafa ya ce akwai gwamnoni da dama da ke shiga cikin rigar mutunci da kuma mashahurancin shugaban kasa Buhari wajen samun goyon bayan al'umma, inda ya buga babban misali da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel