Sallamar Onnoghen: Atiku ya kai korafin Buhari gaban manyan kasashen duniya akan laifuka 5

Sallamar Onnoghen: Atiku ya kai korafin Buhari gaban manyan kasashen duniya akan laifuka 5

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai karar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga manyan kasashen duniya akan sallamar da yayi ma tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku ya kai karan Buhari ne cikin wata wasika daya aika ma gwamnatocin kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da kuma kungiyar kasashen tarayyar turai, inda ya zargi Buhari da kokarin karya tsarin dimukradiyya a Najeriya.

KU KARANTA: Barka: Rahama Sadau ta kammala karatun digiri a wata jami’ar kasar waje

A cewar Atiku, Buhari na yi ma dokokin dimukradiyya kama karya, tare da taka kusoshin hukumomin dimukradiyya da kuma yi ma duk wasu tsare tsareb raba mulkin tsakanin bangarorin gwamnati karan tsaye, duk domin biyan bukatarsa.

Daga cikin zunubban da Buhari ya tafka wadanda Atiku Abubakar ya lissafa ma kasashen wajen sun hada da;

Sallamar Alkalin Alkalai Walter Onnoghen

Sayan jiragen yaki samfurin Tucano

Kaddamar da dokar kwace kudaden sata

Kashe dala biliyan 1 don ayyukan rundunar Sojoji ba tare da neman sahhalewar majalisa ba

Yin watsi da umarnin kotu

Da dai sauransu.

A wani labarin kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin kafatanin Sanatocin Najeriya da suka fito daga jam’iyyar APC, tare da sauran halastattun yan takarar Sanata a inuwar jam’iyyar APC a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja.

A yayin wannan ziyara shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya ma Sanatocin liyafar cin abincin dare, sa’annan ya tattauna dasu game da makomar jam’iyyar APC, musamman game a zaben dake karatowa.

Da yake jawabi a bayan taron, shugaba jam’iyyar APC, kwamared Aliyu Adams Oshiomole ya bayyana cewa taron ya bawa shugaban kasa Buhari damar ganawa da kafatanin Sanatocin jam’iyyar APC dake majalisar dattawa, da kuma yan takarar Sanata a karkashin inuwar jam’iyyar APC da yake sa ran zasu samu nasara a zaben 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel