Dogara ya kulle majalisar wakilai har sai ranar 19 ga watan Feburairu

Dogara ya kulle majalisar wakilai har sai ranar 19 ga watan Feburairu

Majalisar wakilai ta bi sawun takwararta ta dattawa wajen dakatar da duk wasu aikace aikacen majalisa tare da daga cigaba da zaman majalisar har sai bayan zaben 2019, kamar yadda kaakakin majalisar Yakubu Dogara ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin majalisar Yakubu Dogara ya bayyana cewa yan majalisun zasu koma bakin aiki a ranar 19 ga watan Feburairu, kwanaki uku kenan bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisun dokokin Najeriya.

KU KARANTA: Sabon kididdiga ya bayyana jam’iyyar dake da rinjaye a majalisa tsakanin APC da PDP

Dogara ya kulle majalisar wakilai har sai ranar 19 ga watan Feburairu

Majalisar wakilai
Source: Depositphotos

Sai dai kafin majalisar ta tashi, sai da ta kammala aiki akan kudurin dokar karancin albashin ma’aikatan Najeriya, inda ta tabbatar da goyon bayanta ga biyan naira dubu talatin, N30,000 a matsayin karancin albashin ma’aikacin Najeriya.

Haka zalika majalisar ta tattauna tare da tafka muhawara akan kasafin kudin shekarar 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata, inda har sun kai mataki na biyu akan tattaunawar, a yanzu saura matakin karshe ya rage.

Bugu da kari majalisar wakilai ta kammala aiki akan kudurin dokar kafa cibiyar ilimin tsaro ta kasa a babban birnin tarayya Abuja, da kuma kudurin dokar kafa hukumar sufuri ta kasa, daga nan ne kaakakin majalisar ya sanar da dage zaman majalisar.

Tun da fari, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya sanar da dage zaman majalisarsu a makon data gabata, inda ya sanya ranar 19 a matsayin ranar da zasu koma, har ila yau Saraki ya soke gayyatar da yayi ma Sanatoci na su koma majalisa a ranar Talata 29 ga watan Janairu don tattauna batun sallamar tsohon Alkalin Alkalai da shugaba Buhari ya yi.

Sai dai wasu masana siyasar Najeriya sun danganta matakin da Saraki ya dauka na soke gayyatar da yayi ma Sanatocin ga tsoron abinda zai iya faruwa a yayin zaman majalisar, musamman tunda lamarin ya shafi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel