Cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

Cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

A daidai da tsarin Operation Sharan Daji, rundunar sojin kasar na gudanar da ayyuka a mabuyar yan fashi da makami a jihohin Zamfara da Katsina.

Suna gudanar da ayyukan ne tare da hadin gwiwar dukkanin hukumomin tsaro da na yan sa kai domin cimma nasara wajen wanzar da zaman lafiya a jihohin dama kasa baki daya.

A yanzu haka suna gudanar da aiki gano sansanoni da mabuyar yan fashi a yankin sannan kuma su lalata shirin yan ta’addan tare da fatattakarsu.

Ga wasu daga cikin nasarorin da suka samu daga ranar 22 zuwa 29 ga watan Janairu, 2019:

Karanta cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

Kayayyakin da aka kwato daga yan ta'addan
Source: Facebook

Aikin ya samu tarin nasarori. A ranar 22 ga watan Janairu 2019, rundunar da suka gudanar da aikin kakkaba a dajin Gando sun hadu da wasu guggun yan fashi da makami dauke da muggan makamai inda suka sha arangama na tsawon wasu sa’o’i.

Hakan ya tursasa yan fashin barin sansaninsu saboda an sha kansu da wuta a lokacin arangaman. Rundunar sun kuma hadu da wasu yan fashi da ke kan gudanar da aiki a kauyukan Shinkafi, Birnin Magai da wasu kauyukan da aka yasar a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Karanta cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

Kayayyakin da aka kwato daga yan ta'addan
Source: Facebook

Hakazalika, rundunae da ke aiki a jihar Katsina ta yi arangama da wasu yan fashi a wajajen Safana, Runka, Kukan Sama tsakanin ranar 25 zuwa 28 ga watan Janairu, 2019.

An samo abubuwa irin su bindigu, alburusai, ababen hawa, kayayyakin maye da sauransu.

An kuma kashe yan fashi 21 yayinda aka kama 17 da ransu. Rundunar sun kuma lalata wasu sansanoninsu sannan suka ceto mutane 89 da aka yi garkuwa da su, 55 daga cikinsu anyi garkuwa da su ne a aramar hukumar Bukkuyum na jihar Zamfara. An kum sada su da iyalansu.

Karanta cikakken bayani game da Operation Sharan Daji da ke gudana a wasu jihohin Arewa

Kayayyakin da aka kwato daga yan ta'addan
Source: Facebook

Haka kuma an kama wasu masu yiwa yan fashi liken asiri 2 Musa Amadu da Auwalu Mutairu a kauyen Danfumi da ke Birnin Magaji sannan a yanzu haka suna taimakawa sashin kwararru na rundunar.

KU KARANTA KUMA: Murna fal ciki yayinda gwamnatin Sokoto ta shirya raba N1bn bashin kai tsaye ga yan kasuwa

Sannan kuma yan fashin sun kashe yan farin hula 11 da jami’in tsaron sa kai guda a arangamar. Hakalika an yi garkuwa da mutum shida a kauyen Asoula a karamar hukumar Tsafe ba wai a Birnin Magaji kamar yadda wasu kafafen labarai suka rahoto ba.

Manjo Clement Abiade, mukaddashin jami’in bayani na Operatin Sharan Daji ne ya bayar da sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel