Ana wata ga wata: APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin yakin zabe

Ana wata ga wata: APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin yakin zabe

- Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta sanar da sunayen mambobin kwamitin yakin zabenta, domin fuskantar babban zaben watan Fabreru da na Maris da ke gabatowa

- Mr Liman, ya ce jam'iyyar ta kuma zabi Gwamnan jihar, Mr Yari ya zama shugaban kwamitin yakin zaben shugaban kasa karkashin APC

- Ya godewa magoya bayan jam'iyyar APC a jihar bisa hadin kan da suke baiwa shuwagabannin jam'iyyar da ke a jihar

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta sanar da sunayen mambobin kwamitin yakin zabenta, domin fuskantar babban zaben ranar 16 ga watan Fabreru da kuma 2 ga watan Maris da ke gabatowa.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Lawal Liman, ya sanar da hakan ga manema labarai a Gusau a ranar Talata.

Babbar kotun jihar ta 3 da ke da zama a Gusau, karkashin jagorancin Bello Shinkafi, a ranar Laraba ta tabbatar da cewa zaben fitar da gwani da APC ta gudanar ya halasta a jihar karkashin shugabancin Mr Liman.

KARANTA WANNAN: Albarkacin kaza: Yadda gwamnoni suke son shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Marafa

Ana wata ga wata: APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin yakin zabe

Ana wata ga wata: APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin yakin zabe
Source: Twitter

Sai da a wannan ranar ta Juma'a, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da nata hukuncin sabanin na kotun Gusau, inda ta tabbatar da cewa APC bata da 'yan takara a jihar Zamfara, don haka kar INEC ta amince da wasu sunaye daga APC a jihar.

Mr Liman ya ce an raba kwamitocin ne kamar haka: "Babban kwamitin wanda ya kunshi mambobi 60 zai kasance karkashin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar, Abdullahi Abdulkarim.

"Sakataren APC na jihar, Alhaji Sani Musa, zai kasance sakataren kwamitin.

"Sai kuma wani kwamitin na kananan hukumomi wanda ya kunshi mambobi 518.

"A kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomi 14 da ke jihar, akwai mambobi 37 wadanda za su kula da yakin zaben kananan hukumominsu", a cewar Mr Liman cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, jam'iyyar ta kuma zabi Gwamnan jihar, Mr Yari ya zama shugaban kwamitin yakin zaben shugaban kasa karkashin APC.

Ya ce kwamitin na dauke da mambobi 111; inda sakataren gwamntin jihar, Abdullahi Shinkafi zai kasance sakataren kwamitin.

Mr Liman ya godewa magoya bayan jam'iyyar APC a jihar bisa hadin kan da suke baiwa shuwagabannin jam'iyyar da ke a jihar. Kana ya bukace su da sau ci gaba da baiwa jam'iyyar goyon baya domin samar da ababen more rayuwa da bunkasa jihar baki daya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel