Albarkacin kaza: Yadda gwamnoni suke son shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Marafa

Albarkacin kaza: Yadda gwamnoni suke son shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Marafa

- Sanata Kabiru Garba Marafa ya yi ikirarin cewa akwai wasu gwamnoni da ke dogaro da shugaba Buhari da tunanin samun nasarar sake lashe zabe

- Ya ce a lokutan baya, shugaban kasa ne ke dagaro da gwamnoni wajen cin zabe, amma yanzu shugaban kasa Buhari ya canja wannan tarihin

- Sanata Marafa ya yi ikirarin cewa Gwamna Yari na son yin amfani da shugaba Buhari domin cin zabe. Yana son yin amfani da jami'an tsaro domin tafka magudi a zaben

Sanata Kabiru Garba Marafa, (APC, Zamfara) ya yi ikirarin cewa akwai wasu gwamnoni da ke dogaro da shaharar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, da cewar zasu iya samun nasarar sake lashe zabe kasancewar Buharin ya daga hannuwansu, ko domin hakan, jama'a za su zabe su.

A jawabin da ya yi yayin wani taron manema labarai a majalisar tarayya a ranar Talata, ya ce a lokutan baya, shugaban kasa ne ke dagaro da gwamnoni wajen cin zabe, amma yanzu shugaban kasa Buhari ya canja wannan tarihin.

Marafa ya bayyana hakian ne a tsokaci kan hukuncin da babbar kotun Zamfara ta yanke a ranar Juma'ar data gabata, na cewar jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani a jihar, tare da umurtar hukumar zabe ta kasar INEC da ta yi amfani da 'yan takarar da jam'iyyar zata gabatar a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Daga yau na zama cikakken dan PDP, na fice daga jam'iyyar APC - Dogara

Albarkacin kaza: Yadda gwamnoni suke son shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Marafa

Albarkacin kaza: Yadda gwamnoni suke son shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Marafa
Source: Depositphotos

"Ni na san irin kullalliyar da ke a kasa, na san cewa gwamnan na kumfar baki cewar idan har basu yarda da hukuncin kotun ba, APC zata rasa jihar. Sai dai godiya ga Allah, shugaban kasa Buhari zai ci zaben sa a Zamfara koda kuwa babu Yari.

"Na san shugaban kasar na tausasa zuciyarsa ne akan irin abubuwan da ke faruwa a Zamfara, kuma ina da tabbacin cewa zai so wani mutum adali daban ya zo ya shugabanci Zamfara ko da kuwa daga wata jam'iyya ya fito, ma damar APC zata gabatar da wani gurbataccen mutum. Yanzu gwamnoni ne ke dogaro da shugaban kasa zu ci zabe, ba wai akasin hakan ba.

"Yari na son yin amfani da shugaba Buhari domin cin zabe. Yana son yin amfani da jami'an tsaro domin tafka magudi a zaben. Idan kuma karya nake yi, ya bar jam'iyyar APC, sannan ya je ya tsaya a wata jam'iyyar ya ce zai yi takara mu ga idan zai ci."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel