Hukumar gidan kwastam ta tatso Tiriliyan 4 daga 2015 zuwa yanzu – Hameed Ali

Hukumar gidan kwastam ta tatso Tiriliyan 4 daga 2015 zuwa yanzu – Hameed Ali

Shugaban hukuma fasa kauri na kasa watau Hameed Ali ya bayyana cewa sun samu kudin da su ka haura Tiriliyan 4 a cikin shekaru 4. Kanal Ali ya kuma nemi gwamnati tayi kasa da kudin da ake karba wajen shigo da motoci.

Hukumar gidan kwastam ta tatso Tiriliyan 4 daga 2015 zuwa yanzu – Hameed Ali

Shugaban hukumar kwastam yana neman a rage kudin harajin motoci
Source: Depositphotos

Kanal Hameed Ali mai ritaya yace kwastam ta tatsi Naira tiriliyan 4.042 a kan iyakokin kasar nan daga 2015 kawo yanzu. Shugaban hukumar na kwastam yayi wannan jawabi ne a garin Abuja wajen bikin ranar kwastam ta Duniya.

Kudin da hukumar fasa kaurin ta ke samu kullum karuwa yake yi inji Kanal Ali. A cewar sa dai a 2015, kwastam ta iya samun Naira biliyan 904 ne. A 2018 da 2019 kuwa, hukumar ta samu Naira tiriliyan 1.037 da kuma tiriliyan 1.202.

KU KARANTA: Rikicin da ake yi da Gwamnan Gwamnanonin APC yayi kamari

Bayan nan kuma shugaban na kwastam ya nemi a rage kudin harajin da ake karba wajen shigo da sababbin motoci cikin Najeriya daga kashi 70% zuwa akalla kashi 45%. Ali yace yanzu an samu raguwar masu shigo da kaya a sace.

A shekarar ta bara, hukumar ta kwastam mai maganin fasa kauri tayi nasarar damke wasu makamai fiye da 2000 da aka yi kokarin shigo da wasu cikin Najeriya. Bayan haka kuma ta karbe miyugun kwayoyi na tramadol fiye rututu.

Hameed Ali ya fadawa jami’an sa cewa yana sa rai a bana, abin da za su samu ya haura abin da aka samu a bara na Naira tiriliyan 1.2. Jama’a da dama dai sun yaba da irin aikin da Ali yake yi a NCS.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel