Murna fal ciki yayinda gwamnatin Sokoto ta shirya raba N1bn bashin kai tsaye ga yan kasuwa

Murna fal ciki yayinda gwamnatin Sokoto ta shirya raba N1bn bashin kai tsaye ga yan kasuwa

- Gwamnatin jihar Sokoto na shirin raba naira biliyan 1 ga yan kasuwa da ke jihar a matsayin bashin kai tsaye

- Gwamna Tambuwal ne ya bayyana wannan yunkuri, inda yace bashin baya daga cikin naira biliyan 2 na farko da aka fara rarrabawa ma’aikata

- Gwamnatin ta kuma dakatar da karban riba akan basussukan wanda za a biya bayan shekaru biyu

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin Aminu Tambuwal na jihar Sokoto na shirin raba naira biliyan 1 ga yan kasuwa da ke jihar a matsayin bashin kai tsaye.

Gwamnan ne ya bayyana wannan yunkuri, inda a cewarsa bashin baya daga cikin naira biliyan 2 na farko da aka fara rarrabawa ma’aikata.

Gwamnan yayi bayanin cewa kwanan nan za a fara rarraba bashin naira biliyan 2 na farko da gwamnatinsa ta amince da shi ga wadanda za su amfana da zaran sun cika ka’idojin da aka shimfida.

Murna fal ciki yayinda gwamnatin Sokoto ta shirya raba N1bn bashin kai tsaye ga yan kasuwa

Murna fal ciki yayinda gwamnatin Sokoto ta shirya raba N1bn bashin kai tsaye ga yan kasuwa
Source: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa Tambuwal yayi Magana ne a wani taron tattaunawa tare da mambobin yan kasuwa a jihar Sokoto.

Majalisar ciniki na jihar tare da hadin gwiwar kungiyar yan kasuwa na Sokoto ne suka shirya taron tattaunawar.

Gwamnan yace za a samar da naira biliyan dayan ne ta kamfanonin zuba jari na jihar, majalisar ciniki da kuma kungiyar yan kasuwa na Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC

A cewarsa, gwamnatin jihar ta tsawaita adadin lokacin da za a iya bashin daga shekara daya zuwa shekara biyu.

Gwamnatin ta kuma dakatar da karban riba akan basussukan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel