Sabon kididdiga ya bayyana jam’iyyar dake da rinjaye a majalisa tsakanin APC da PDP

Sabon kididdiga ya bayyana jam’iyyar dake da rinjaye a majalisa tsakanin APC da PDP

Kididdiga da jaridar Premium Times ta yi ta nuna har yanzu jam’iyyar APC ce kda rinjaye a tsakanin wakilan yan Najeriya dake majalisar dattawa, wanda aka fi sani da suna Sanatoci, sai dai rinyajen ba wani mai gwabi bane, amma kuma dan siyasa baya raina kuri’a ko da guda daya ce.

Majiyar Legit.ng ta gudanar da wannan kididdiga ne duba da yawan sauyin sheka da ake samun rahoto da wasu Sanatocin ke yi, musamman a shekarar data gabata inda shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya fice daga AP zuwa PDP.

KU KARANTA: Sanatocin APC da yan takaran Sanata sun ziyarci Buhari a fadar Villa

Wani muhimmin bayani daya kamata mai karatu ya sani shine akwai Sanatoci guda dari da tara, 109, ne a majalisar dattawan Najeriya, inda ake samun sanatoci guda uku daga kowacce jahar Najeriya sai babban birnin tarayya Abuja dake da Sanata guda daya rak.

Amma sakamakon wannan sabon kididdiga ya nuna jam’iyyar APC ce kan gaba wajen adadin Sanatoci a majalisar dattawa, inda take da Sanatoci guda hamsin da shida, 56, yayin da jam’iyyar PDP keda Sanatoci arba’in da bakwai, 47.

Idan aka hada lissafin 56 da 47 zai bayar da adadin Sanatoci 103, sauran Sanatoci shida sun warwatsu a tsakanin jam’iyyun APGA, SDP da PRP dake da Sanat guda guda, sai jam’iyyar ADC dake da Sanatoci uku.

Sabon kididdiga ya bayyana jam’iyyar dake da rinjaye a majalisa tsakanin APC da PDP

Majalsa
Source: Depositphotos

Idan za’a tuna a farkon mulkin shugaba Buhari, jam’iyyar APC na da Sanatoci sittin da hudu ne, 64, yayin da jam’iyyar PDP ke da Sanatoci hamsin, 50, amma a shekarar data gabata an samu sauyin sheka da dama, inda a zuwa daya Sanatocin APC 15 suka fice daga cikinta zuwa PDP da ADC.

Ga jerin Sanatocin nan da jam’iyyunsu daki daki;

1. Jahar Abia

Theodore Orji PDP

Enyinnaya Abaribe PDP

Mao Ohuabunwa PDP

2. Jahar Adamawa

Abdul-Aziz Nyako ADC

Binta Masi Garba APC

Ahmad Abubakar APC

3. Jahar Akwa Ibom

Godswill Akpabio APC

Nelson Effiong APC

Bassey Akpan PDP

4. Jahar Anambra

Stella Oduah PDP

Andy Uba APC

Victor Umeh APGA

5. Jahar Bauchi

Lawan Gumau APC

Sulaiman Nazif PDP

Isah Misau PDP

6. Jahar Bayelsa

Ben Murray-Bruce PDP

Emmanuel Paulker PDP

Foster Ogola PDP

7. Jahar Benue

Barnabas Gemade SDP

George Akume APC

David Mark PDP

8.Jahar Borno

Ali Ndume APC

Abubakar Kyari APC

Baba Garba APC

9. Jahar Cross River

Gershom Bassey PDP

John Enoh APC

Rose Okoji Oko PDP

10. Jahar Delta

Peter Nwaboshi PDP

Ovie Omo-Agege APC

James Manager PDP

11. Jahar Ebonyi

Obinna Ogba PDP

Sunday Ogbuoji APC

Sam Ominyi Egwu PDP

12. Jahar Edo

Francis Alimikhena APC

Matthew Urhoghide PDP

Ordia Clifford PDP

13. Jahar Ekiti

Duro Faseyi PDP

Fatimat Raji-Rasaki APC

Biodun Olujimi PDP

14. Jahar Enugu

Gilbert Nnaji PDP

Ike Ekweremadu PDP

Utazi Chukwuka PDP

15. Jahar Gombe

Danjuma Goje APC

Joshua Lidani APC

Usman Nafada PDP

16. Jahar Imo

Hope Uzodinma APC

Samuel Anyanwu PDP

Ben Uwajumogu APC

17. Jahar Jigawa

Muhammed Ubali Shitu PDP

Abdullahi Gumel APC

Mohammed Sabo APC

18. Jahar Kaduna

Shehu Sani PRP

Suleiman Hunkuyi PDP

Danjuma Laah PDP

19. Jahar Kano

Jibrin I. Barau APC

Kabiru Gaya APC

Rabiu Kwankwaso PDP

20. Jahar Katsina

Kurfi Umaru APC

Abu Ibrahim APC

Ahmad Babba-Kaita APC

21. Jahar Kebbi

Adamu Aliero APC

Bala Naallah APC

Yahaya Abdullahi APC

22. Jahar Kogi

Ahmed Ogembe PDP

Atai AIidoko Ali PDP

Dino Melaye PDP

23. Jahar Kwara

Shaaba Lafiagi PDP

Rafiu Ibrahim PDP

Bukola Saraki PDP

24. Jahar Lagos

Gbenga Ashafa APC

Oluremi Tinubu APC

Olamilekan Adeola APC

25. Jahar Nasarawa

Philip Aruwa Gyunka PDP

Suleiman Adokwe PDP

Abdullahi Adamu APC

26. Jahar Niger

David Umaru APC

Sani Mohammed APC

Aliyu Sabi Abdullahi APC

27. Jahar Ogun

Olanrewaju Tejuoso APC

Buruji Kashamu PDP

Gbolahan Dada APC

28. Jahar Ondo

Omotayo Alasoadura APC

Robert Boroffice APC

Yele Omogunwa APC

29. Jahar Osun

Olusola Adeyeye APC

Omoworare Babajide APC

Ademola Adeleke PDP

30. Jahar Oyo

Abdulfatai Buhari APC

Rilwan Akanbi ADC

Monsurat Sunmonu ADC

31. Jahar Plateau

Jeremiah Useni PDP

Johan Jang PDP

Joshua Dariye APC

32. Jahar Rivers

Magnus Abe APC

Andrew Uchendu APC

Osinakachukwu Ideozu APC

33. Jahar Sokoto

Ibrahim Danbaba PDP

Aliyu Wamakko APC

Ibrahim Gobir APC

34. Jahar Taraba

Emmanuel Bwacha PDP

Abubakar Sani PDP

Yusuf Abubakar Yusuf APC

35. Jahar Yobe

Ahmed Lawan APC

Mohammed Hassan APC

Bukar Ibrahim APC

36. Jahar Zamfara

Tijjani Kaura APC

Kabir Garba APC

Ahmad Sani PDP

37. Abuja

Philip Aduda Tanimu PDP

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel