Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC

Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC

- Kungiyar NLC ta bayyana cewa gwamnonin jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci

- Kungiyar ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi watsi da shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na biyan N27,000 a matsayin karancin albashi

- A halin da ake ciki, majalisar wakila

Kungiyar kwadago na Najeriya (NLC) a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu a Abuja ta bayyana cewa gwamnonin jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci.

Kungiyar ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi watsi da shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na biyan N27,000 a matsayin karancin albashi.

Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC

Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC
Source: Depositphotos

NLC ta yi wannan roko ne a wani taron tattaunawa na majalisar dokoki akan dokar.

Kungiyar ta yi watsi da N27,000 da gwamnati ta gabatar.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya fada ma mambobin majalisar dokokin a wajen taron cewa N30,000 shine abunda NLC ta tsaya akai kuma tana nan akan bakarta.

Mista Wabba yace NLC ta amince da wannan adadin ne saboda kawo karshen kace-nacen da ake tayi.

A halin da ake ciki, Majalisar wakilai ta isar da dokar kara mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

KU KARANTA KUMA: Malami ya tura jerin laifukan da suke zargin Onnoghen da aikatawa ga Majalisar alkalai

Majalisar ta isar da dokar ne bayan duba rahoton da kwatinta na wucin-gadi ya gabatar a lokacin zaman majalisar na ranar Talata, 29 ga watan Janairu.

Gabatarwar na zuwa ne kimanin mako guda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika dokar karancin albashin don aiwatar da shi, biyo bayan amincewar majalisar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel