Malami ya tura jerin laifukan da suke zargin Onnoghen da aikatawa ga Majalisar alkalai

Malami ya tura jerin laifukan da suke zargin Onnoghen da aikatawa ga Majalisar alkalai

Rahotanni da ke billowa daga jaridar The Cable ta yi ikirarin cewa ofishin Atoni-janar na tarayya ta tura jerin zarge-zargen da aka yiwa dakataccen Shugaban alkalan Najeriya Walter Onnoghen zuwa ga majalisar alkalai na kasar (NJC).

Rahoton ya ci gaba da ikirarin cewa wani na kusa da ma’aikatar shari’a yace taardar korafin na dauke da adadin zarge-zargen da ake yiwa Shugaban alkalan, ciki harda jawaban bnki da kuma na kadarorin da aka gano suna da nasaba da shi.

Malami ya tura jerin laifukan da suke zargin Onnoghen da aikatawa ga Majalisin alkalai

Malami ya tura jerin laifukan da suke zargin Onnoghen da aikatawa ga Majalisin alkalai
Source: Depositphotos

Wani babban jami’in ma’aikatar yace: “Kotun kula da da’ar ma’aikata ba ta gabatar da wadannan zarge-zargen akan alkalin alkalan a kotun ba saboda lamari ne na daban daga rashin kaddamar da kadarorinsa.

“Ana ta dasa alamomin tambaya game da ka’idar dakatar da Onnoghen da Shugaban kasar yayi, amma sashi na 11 na dokar kasar ya nuna karara cewa duk wanda ke rike da karfin ikon nada mukami yana da karfin ikon yin hukunci. Mun yarda cewa Shugaban kasar ya yi hukunci ne daidai da dokar kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi

“Baya ga haka, anyi cikakken bincike akan manyan zarge-zargen a yanzu. Wadannan zarge-zarge na da alaka da wasu dukiyoyi da ba bayyanannu bane.

“An tura komai ga kungiyar NJC domin ta gudanar ayyukanta sannan ta bari Onnoghen ya fuskanci hukunci. Wannan wani abune na daban daga shari’an rashin kaddamar da kadarorinsa a gaban CCT.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel