Yanzu-yanzu: Gwamnonin Najeriya sun shiga ganawar sirri da IGP Adamu da NSA Munguno kan zaben 2019

Yanzu-yanzu: Gwamnonin Najeriya sun shiga ganawar sirri da IGP Adamu da NSA Munguno kan zaben 2019

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF tana cikin ganawar sirri da mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Munguno, da sifeto janar na hukumar yan sanda, IGP Adamu Mohammed, a sakatariyanta dake birnin tarayya Abuja.

Kanal Babagana Munguno ya gayyaci gwamnonin ganawar ne domin musu bayani kan yanayin tsaron kasa gabanin zaben da zai gudana nan da kwanaki 17.

Bisa ga bincike, ana wannan ganawar ne domin gamsar da gwamnoni kan matakan da ake shirin dauka na tabbatar da zabe cikin zaman lafiya da lumana.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi

A bangare guda, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tabbatar da ya sadu da shugaban tsaro na kasar don tabbatar da zabe cikin zaman lafiya a jihar ta Kaduna.

A jawabin da yayi a taron da yayi da masu ruwa da tsaki a garin Kafanchan, Babban birnin karamar hukumar Jema'a, Gwamnan ya bayyana cewa bayanin leken asiri na kwanan nan ya nuna cewa akwai mutanen da ke da burn tada husuma a kudancin Kaduna kafin ko lokacin zabe.

Kamar yanda yace, rahoton ya nuna cewa masu shiryawan naso hatsaniyar ta watsu har zuwa sauran sassan jihar saboda sun hango faduwar su a zabe mai zuwa.

"Na sadu da shugaban tsaro Janar Abayomi Olanisakin, shugaban jami'an sojin Najeriya Lt janar Tukur Buratai da kuna sifeta janar na yan sanda Mohammed Abubakar Adamu akan zancen kuma sunyi min alkawarin karfafa tsaro a jihar Kaduna kafin da kuma lokacin zabe," gwamnan ya bayyana.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel