Daga yau na zama cikakken dan PDP, na fice daga jam'iyyar APC - Dogara

Daga yau na zama cikakken dan PDP, na fice daga jam'iyyar APC - Dogara

- Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya fito fili daga karshe, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP

- Ya sanar da sauya shekarsa zuwa PDP tare da wasu 'yan majalisu guda biyu, Edward Pwajok da kuma Ahmed Yerima

- Mr. Dogara, wanda ya dade yana takun saka da gwamnan jiharsa, Mohammed Abubakar, ya dade yana yunkurin ficewa daga APC zuwa PDP, kamar yadda rahotanni suka bayyana

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya fito fili daga karshe, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Kakakin majalisar ya sanar da sauya shekarsa a zaman majalisar wakilan tarayyar na ranar Talata. Ya sanar da sauya shekarsa zuwa PDP tare da wasu 'yan majalisu guda biyu, Edward Pwajok da kuma Ahmed Yerima.

Dogara, a watan Satumbar 2018 ya kawo karshen jita jitar da ake yadawa na cewar ya fice daga APC zuwa PDP a lokacin da ya ziyarcu sakatariyar sabuwar jam'iyyarsa da ke Abuja inda ya mayar da fom din takararsa ta kujerar majalisar wakilan tarayya.

KARANTA WANNAN: Gabanin zabe: Yadda kasafin 2019 ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilan tarayya

Daga yau na zama cikakken dan PDP, na fice daga jam'iyyar APC - Dogara

Daga yau na zama cikakken dan PDP, na fice daga jam'iyyar APC - Dogara
Source: Twitter

Wannan mataki nasa ya biyo mako daya bayan da daruruwan magoya bayansa daga kananan hukumomin da ya ke wakilta na Dass/Tafawa Balewa/Bogoro da ke jihar Bauchi, inda suka gabatar masa da fom din tsayawa takara, tare da bukatarsa da ya bar jam'iyyar APC.

Mr. Dogara, wanda ya dade yana takun saka da gwamnan jiharsa, Mohammed Abubakar, ya dade yana yunkurin ficewa daga APC zuwa PDP, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ba kamar sauran mambobin majalisun tarayya ba wadanda suka bayyanawa duniya ficewarsu daga wata jam'iyya zuwa wata ba tare da bata lokaci ba, shi Mr Dogara, ya ki bayyana hakan, har sai a zaman karshe na majalisar kafin zaben 2019.

Da ya ke jawabi a ofishin PDP a wancan lokaci, Mr Dogara ya ce ya fice daga APC tare da cewa APC a Bauchi ta yaudari al'ummar jihar na gaza cika alkawura da ta daukarwa jama'a, domin hakan ne kuma ya sanya shi ficvewa daga jam'iyyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel