Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi

- Majalisar wakilai ta gabatar da dokar kara mafi karancin albashin ma’aikata na kasa

- Ta isar da dokar ne bayan duba rahoton da kwatinta na wucin-gadi ya gabatar a lokacin zaman majalisar na ranar Talata

- Kwamitin ta amince da N30,000 ga ma’aikata a mataki tarayya da jiha

Majalisar wakilai ta isar da dokar kara mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

Majalisar ta isar da dokar ne bayan duba rahoton da kwatinta na wucin-gadi ya gabatar a lokacin zaman majalisar na ranar Talata, 29 ga watan Janairu.

Gabatarwar na zuwa ne kimanin mako guda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika dokar karancin albashin don aiwatar da shi, biyo bayan amincewar majalisar kasar.

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta gabatar da dokar karancin albashi
Source: Depositphotos

Majalisar Shugaban kasar ta amince da N27,000 yayinda gwamnatin tarayya tace za ta kara kudin zuwa N30,000 ga ma’aikatanta.

Amma yayin aiwatar da dokar, yan majalisar sun yanke shawarar barin karancin albashin kamar yadda kwamitin tayi shawara.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar gwamna na ANRP a Kebbi ya janye daga tseren, ya koma APC

Kwamitin ta amince da N30,000 ga ma’aikata a mataki tarayya da jiha.

Sun kuma yanke shawarar cewa dokar zai fara aiki daga ranar da Shugaban kasar yayi umurni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel