Gabanin zabe: Yadda kasafin 2019 ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilan tarayya

Gabanin zabe: Yadda kasafin 2019 ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilan tarayya

- Majalisar wakilan tarayya, a zamanta na ranar Talata, ta kada kuri'a inda kudirin kasafin kudin kasar na 2019 ya wuce karatu na biyu

- Bayan kammala kada kuri'a tare da wucewar kasafin, kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya mika shi zuwa ga kwamitin kasafi na majalisar

- A makon da ya gabata ne majalisar ta soma tafka muhawara kan kasafin wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar

Mambobin majalisar wakilan tarayya sun amince kasafin kudin kasar na 2019 ya wuce karatu na biyu.

Kasafin kudin ya wuce karatu na biyu ne a ranar Talata a zaman majalisar wakilan tarayyar karkashin shugabancin kakakin majalisar wakilan tarayyar, Yakubu Dogara.

Kakakin majalisar, a yayin da ya gabatar da kudin kasafin gaban majalisar domin kada kuri'a, ya kuma mika shi zuwa ga kwamitin kasafi da sauran lamura masu muhimmanci da kuma sauran kwamitoci.

KARANTA WANNAN: Fashi da rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta bukaci al'umar jihar su yi azumin kwanaki 3

Gabanin zabe: Yadda kasafin 2019 ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilan tarayya

Gabanin zabe: Yadda kasafin 2019 ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilan tarayya
Source: Depositphotos

A makon da ya gabata ne majalisar ta soma tafka muhawara kan kasafin wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar.

Shugaban kasa Buhari ya gabatarwa hadin guiwar majalisar dokokin kasar kasafin 2019 a ranar Laraba, cikinn watan Disamba, 2018, wanda ke dauke da N8.83trn

Kasafin kudin wanda ya nuna kashi daya cikin hudu da ya kai N2.14trn za a batar da su ne wajen biyan basussuka yayin da ake sa ran bangaren gine gine da sabbin ayyuka zai lakume N4.04trn.

Bangaren kammala ayyukan da tuni aka fara, da kuma gyare gyare kuwa kamar yadda shugaban kasar ya gabatar zai lakume N2.031trn.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel