An kama daruruwan katunan zabe hannun wasu gungun jama'a a Akwa Ibom

An kama daruruwan katunan zabe hannun wasu gungun jama'a a Akwa Ibom

- Hukumar NDLEA reshen jihar Akwa Ibon tace ta kama mutane 120 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi

- A samamen da suka kai ne suka kama wani mutum da katikan zabe 244

- An kama wadanda ake zargin da tsabar kudi har Naira 301,000

An kama daruruwan katunan zabe hannun wasu gungun jama'a a Akwa Ibom

An kama daruruwan katunan zabe hannun wasu gungun jama'a a Akwa Ibom
Source: UGC

NDLEA ta jihar Akwa Ibom a ranar Monday tace ta kama mutane 120 da ake zargi tare da miyagun kwayoyi a samamen shirye shiryen zabe da sukayi tsakanin Satumba 2018 da Janairu 2019.

Kwamandan jihar na NDLEA, Mr Mohammed Sokoto, ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai akan aiyukan cibiyar a Uyo a ranar talata.

Sokoto yace a lokacin, ofishin su ya kwace kilogram 51 na cannabis, gram 250 na wuiwi, gram 17 na hodar iblis da gram 500 na tramadol, diezepam da polypro.

"Al'ada ce idan zabe ya gabato, NDLEA kan kai samame don shirin zabe don tabbatar da anyi zabe cikin lumana. Munsan kwayoyo na assasa aikata laifuka. A saboda haka, mun kai samame guraren siyar da miyagun kwayoyi a jihar."

"A wannan lokacin ne muka kama mutane 120 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi kuma ana bincike."

"Matasa balle samari da yammata zasu iya kirkiro matsaloli da zasu iya tarwatsa zabe kuma a saboda haka ne NDLEA ta fito don tabbatar da hana aikata laifuka yanda za'ayi zabe mai cike da yanci da zaman lafiya."

DUBA: Bayan janyewar Oby Ezekwesile, sauran kananun ‘yan takara da suka karaya sun Kanye zasu mara wa daya baya

"Wata Joy Monday Adams gagararriyar mai safarar miyagun kwayoyi a jihar, an kamata da gram 239 na wuiwi kuma an kaishi kotu. A yanzu haka tana gidan kaso kafin a cigaba da shari'ar a sati mai zuwa. Kudi Naira 301,000 ne aka samu a gurin masu safarar kwayoyin " inji Sokoto.

Shugaban yace a daya daga cikin samamen nasu na ranar juma'a, sun kama wani Prince Okon Bassey dauke da katin zabe na dindindin guda 244 mallakin mutane daban daban.

Sokoto yace an mika wanda ake zargin ga hukumar zabe mai zaman kanta don cigaba da bincike.

"Wannan ya nuna cewa bincike tare da kama masu safarar miyagun kwayoyi kan iya bankado sauran laifuka tare da kama yan ta'addan."

GA WANNAN: Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

Shugaban ya hori mutanen jihar Akwa Ibom da su cigaba da gujewa miyagun kwayoyi tare da bin doka.

Ya jaddada cewa tsaron kasar nan kada a barshi a hannun gwamnati da cibiyoyin tsaro kadai.

Ya shawarci mutane dasu mika duk wani labarin masu safarar miyagun kwayoyi ga hukumar, tare da tabbatar wa zasu kare wanda ya kawo labarin.

A hakan ne kwamshinan zaben jihar Mr Mike Igini yace katukan zaben na hannun hukumar zaben kuma an mika wanda ake zargi ga yan sanda don cigaba da bincike.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel