Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

- Biliyoyi ake hana masu fansho bayan wasu sun gano akwai kudi a asusun

- Fansho shine kudin da ma'aikata suka tara don ci lokacin da karfinsu ya kare

- Hukumar Fansho sunanta PenCom. Pension Commission kenan

Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018
Source: Depositphotos

Kudin Fansho dai hakkoki ne na ma'aikata da suke ajje ake tara wa har zuwa lokacin ritaya, lokacin da karfin mutum ya kare, sai ya ci a hankali har tsufa. Sai dai mahandama sun riga sun gano akwai kudi maqare da ma'aikatan Najerya suka tara, kuma sun ta kokarin cinye wa.

Hukumar PenCom, tace a tsakiya zuwa karshen bara kadai, ta kwato kusan rabin Tiriliyan na Nairori na hakkokin masu tara fansho daga kamfunna da suka ki biya cikin asusun masu yi musu aiki, lamari da ya zama wata hobbasa ta tabbatar da adalci.

GA WANNAN: Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

Hukumar ce ta saki haka a rahotonta na karshen bara, wanda ya nuna ta kwato N564.67m daga wadannan ma'aikatu da bassu biya a asusun inda ake tara wa ma'aikata.

Tace ta dauki masu bin kadi da binke, inda suka tabbatar an tauye wadannan hakkoki kuma ta karbi harda kudinn ruwa da ma na tara saboda makarar da suka yi, wanda ya kama N199.01 million da N365.67 million.

Ma'aikata dai zasu dara da wannan lamari, sai dai suna kuma ganin ya kamata ace suna morar wannan kudi tun yanzu, ba lallai ma sai karfinsu ya kare ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel