Dan takarar gwamna na ANRP a Kebbi ya janye daga tseren, ya koma APC

Dan takarar gwamna na ANRP a Kebbi ya janye daga tseren, ya koma APC

- Dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar Abundant Nigeria Renewal Party (ANRP) a jihar Kebbi, Alhaji Mustaph Yauri, ya janye daga tseren kujerar gwamna

- Mustapha Yauri ya kuma sanar da komawarsa jam'iyyar All Progressive Congress (APC)

- Yace APC na da duk wata dama na lashe zabe a jihar Kebbi dama kasa baki daya duba ga hanyar da shugabancinta ya dosa da kuma tarin kokari da tayi cikin shekaru uku da suka gabata

Dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar Abundant Nigeria Renewal Party (ANRP) a jihar Kebbi, Alhaji Mustapha Yauri, ya janye daga tseren kujerar gwamna ya koma jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

Yayinda yake jawabi bayan wani ganawar sirri da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ofishin hukumar da ke Birnin Kebbi, yace ya yanke shawarar janyewa daga tseren ne ga APC saboda labari mai kyau da ya samu na ayyukan ci gaba da Gwamna Atiku Bagudu ya faro a jihar.

Dan takarar gwamna na ANRP a Kebbi ya janye daga tseren, ya koma APC

Dan takarar gwamna na ANRP a Kebbi ya janye daga tseren, ya koma APC
Source: Facebook

Ya bukaci magoya bayansa da su bar jam’iyyar ANRP sannan su koma jam’iyyar APC tare da shi.

Tsohon dan takarar gwamnan na ANRP ya kara da cewa kafin ya yanke shawarar barin jam’iyyar, ya tattauna da manyan masu ruwa da tsaki a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yan takarar Shugaban kasa sun marawa Buhari baya akan dakatar da Alkalin-alkalai

“Kokarin da gwamnatin APC ta yi a jihar da ma a matakin tarayya ya sanya ni daukar wannan hukunci,” inji shi.

Yace APC na da duk wata dama na lashe zabe a jihar Kebbi dama kasa baki daya duba ga hanyar da shugabancinta ya dosa da kuma tarin kokari da tayi cikin shekaru uku da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel