Fashi da rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta bukaci al'umar jihar su yi azumin kwanaki 3

Fashi da rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta bukaci al'umar jihar su yi azumin kwanaki 3

- Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga daukacin al'umma da su gudanar da azumin kwanaki ukku da kuma addu'o'i na rokon Allah ya kawo karshen tashe tashen hankulan a jihar

- A cewarsa, azumi da addu'o'in zai taimaka matuka saboda na tabbata in ba ta wannan bangaren ba, ta wani bangaren, rikicin ya shafi kowa

- Kwamishinan ya ce har yanzu dokar nan ta haramta safarar itatuwa, gawayi da kuma sayar da fetur ba bisa ka'ida ba na nan a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga daukacin al'ummar jihar da su gudanar da azumin kwanaki ukku da kuma yin addu'o'i na rokon Allah ya kawo karshen tashe tashen hankulan da ke faruwa a jihar musamman fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da dai sauransu.

Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar, Bello Dankade, ya yi wannan kiran a lokacin taron manema labarai a ranar Talata a Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce: "Ina da tabbacin cewa kuna sane da irin namijin kokarin da gwamnatin jihar da ta tarayya ke yi na magance matsalolin tsaro a jihar."

KARANTA WANNAN: A farke ko a cikin barcina, Nigeria ce ke mun yawo a cikin kwakwalwata - Buhari

Fashi da rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta bukaci al'umar jihar su yi azumin kwanaki 3

Fashi da rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta bukaci al'umar jihar su yi azumin kwanaki 3
Source: Twitter

A cewarsa, azumi da addu'o'in zai taimaka matuka, domin rokon Allah ya shiga cikin lamuran jihar musamman a bangaren kare rayuka da kuma baiwa jami'an tsaro nasarar kawo karshen 'yan ta'addan da suka addabi jihar.

"Ya kamata ace dukkanin daukacin al'ummar Nigeria su gudanar da wannan azumin saboda na tabbata in ba ta wannan bangaren ba, ta wani bangaren, rikicin ya shafi kowa.

"Haka zalika muna rokon maluman islamiyoyi dana tsangaya da su taimaka wajen sauke Al-Qur'ani mai girma a makarantunsu tare da dalibansu, domin neman taimakon Allah."

Kwamishinan ya ce har yanzu dokar nan ta haramta safarar itatuwa, gawayi da kuma sayar da fetur ba bisa ka'ida ba na nan a jihar, yana mai cewa karya dokar na iya sawa mutum ya fuskanci fushin hukuma.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel