Dalilin da ya sa Buhari ya gana da sanatocin APC – Oshiomhole

Dalilin da ya sa Buhari ya gana da sanatocin APC – Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya bayyana ainahin dalilin da yasa shugaba Buhari ya gana da sanatocin APC

- Oshiomhole yace an shirya taron ne domin shugaban kasar ya samu damar ganawa da sanatoci da yan takarar kujerar sanata na jam'iyyar kai tsaye

- Ya nuna yakinin cewa yan Najeriya za su ba APC mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawa da majalisar wakillai a zabe mai zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 28 ga Janairu ya karbi bakuncin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da yan takara zuwa wani taron cin abinci a fadar Shugaban kasa, da ke Abuja.

Da yake Magana da manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan taron cin abincin, Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya bayyana taron a matsayin “haduwa mai kyau”.

Ya ce taron ya samar da wani dama ga Shugaban kasa wajen haduwa da masu ruwa da tsaki na majalisar dattawa da kuma “sanatoci masu zuwa” wato yan takarar kujerar maalisar dattawa.

Dalilin da ya sa Buhari ya gana da sanatocin APC – Oshiomhole

Dalilin da ya sa Buhari ya gana da sanatocin APC – Oshiomhole
Source: Facebook

Mista Oshiomhole ya nuna yakinin cewa yan Najeriya za su ba APC mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawa da majalisar wakillai a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Onnoghen: Sanatocin APC a majalisar dattawa sun kalubalanci Saraki, sun yi adawa da kai Buhari kotu

Yace: “An yi zaben ne musamman don Shugaban kasar ya gana da masu ruwa da tsaki na majalisar dattawa da kuma sanatoci masu zuwa da ikon Allah.

“Hikimar yin hakan shine don Shugaban kasar ya samu damar ganawa kai tsaye da sanatoci da yan takarar kujerar sanata a APC don su yi aiki sosai wajen tabbatar da cewar sun samu nasara a zabe mai zuwa.

“Wannan shine daman a farko da wasu yan takarar sanata suka samu na ganawa da Shugaban kasar.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel