Yan takarar Shugaban kasa sun marawa Buhari baya akan dakatar da Alkalin-alkalai

Yan takarar Shugaban kasa sun marawa Buhari baya akan dakatar da Alkalin-alkalai

- Yan takarar Shugaban kasa karkashin lemar kungiyar FPCPPGG sun ce suna tare da shugaba Buhari akan dakatar da Shugaban alkalan kasar

- Shugaban kungiyar, Alhaji Shittu Muhammed Kabiru yayi korafin cewa tsige Onnoghen ba zai shafi zaben 2019 ba

- Ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta kalli matakin da Shugaban kasar ya dauka don ci gaban Najeriya ba wai don wani son zuciyarsa ba

Yan takarar Shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019, karkashin lemar kungiyar FPCPPGG sun ce shugaba Muhammadu Buhari na da goyon bayansu akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

Shugaban kungiyar, Alhaji Shittu Muhammed Kabiru wanda ya bayyana matsayar kungiyar a jiya a wani taron manema labarai a Abuja, yayi korafin cewa tsige Onnoghen ba zai shafi zaben 2019 ba.

Alhaji kabiru ya bayyana cewa laifin da ake zargin Justis Onnoghen da aikatawa ba wai laifi na shari’a bane, inda ya kara da cewa matakin da Buhari ya dauka dakatarwa ne kawai ba wai tsige shi aka yi gaba daya ba wanda da shine zai ja hankalin kungiyar masu shari’a na kasa.

Yan takarar Shugaban kasa sun marawa Buhari baya akan dakatar da Alkalin-alkalai

Yan takarar Shugaban kasa sun marawa Buhari baya akan dakatar da Alkalin-alkalai
Source: UGC

Ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta kalli matakin da Buhari ya dauka don ci gaban Najeriya ba wai don wani son zuciyarsa ba.

A baya mun ji cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dattawa sun janye mambobinsu daga wani kara da majalisar ta shigar akan batun dakatar da Walter Onnoghen, Shugaban alkalan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari

A wani jawabi dauke da sa hannun Ahmed Lawan, Shugaban majalisa, a daren ranar Litinin, 28 ga watan Janairu jiga-jigan jam’iyyar sunce ba su gana don yanke wannan hukunci ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel