Onnoghen: Lauyoyi sun bijirewa umurnin kungiyar NBA na hana su shiga kotu

Onnoghen: Lauyoyi sun bijirewa umurnin kungiyar NBA na hana su shiga kotu

- Rahotanni sun bayyana cewa lawyoyi sun halarci dakunan sauraron shari'a, duk da umurnin da kungiyar lauyoyi ta kasa (nba) ta ba su na kauracewa shiga kotunan

- Ana ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum a babbar kotun gwanatin tarayya da kuma babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke Maitama

- Da yawa daga cikin kotunan da ke a babbar kotun gwamnatin tarayya sun cika da lauyoyin a zaman jiran fara sauraron shari'o'i da suke yi

Rahotanni sun bayyana cewa lawyoyi da ke a babban birnin tarayya Abuja sun halarci dakunan sauraron shari'a da ke cikin kotuna daban daban na birnin, duk da umurnin da kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta ba su na kauracewa shiga kotunan.

Kungiyar ta yi kira ga mambobinta da su kauracewa duk wani aiki da ya shafi shiga kotu a karshen taron majalisar zartaswa na kungiyar da ta gabatar a ranar Litinin, wanda aka tattauna akan batun dakatar da Walter Onnoghen, daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa.

A ranar Juma'ar da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Mr Onnoghen biyo bayan karar da aka shigar da shi, kan zargin boye wasu makudan kudaden kasashen waje da ya mallaka kamar yadda kotun kundin dokar kasar ya bukata.

KARANTA WANNAN: Sarauta cikin siyasa: Atiku ya samu saurautar Obong Emem na jihar Akwa Ibom

Onnoghen: Lauyoyi sun bijirewa umurnin kungiyar NBA na hana su shiga kotu

Onnoghen: Lauyoyi sun bijirewa umurnin kungiyar NBA na hana su shiga kotu
Source: UGC

Wannan dakatarwar ana kallonta a matsayin hukuncin da ya sabawa dokar kasar, wanda kuma ya jawo cece kuce a cikin kasar dama kasashen ketare. Kungiyar NBA ta umurci a rufe kotuna a cikin jerin zanga zangar da ta gudanar, wanda ke nuna tsantsar damuwarsu kan karya dokar fannin shari'a ta kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum a babbar kotun gwanatin tarayya da kuma babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke Maitama, a yayin da lauyoyin suka halarci zaman kotunan.

Da yawa daga cikin kotunan da ke a babbar kotun gwamnatin tarayya sun cika da lauyoyin a zaman jiran fara sauraron shari'o'i da suke yi.

Cikakken rahoton na zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel