Yanzu-yanzu: Yayinda ake sauraron zuwan Buhari a Abia, anyi garkuwa da shugaba jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Yayinda ake sauraron zuwan Buhari a Abia, anyi garkuwa da shugaba jam'iyyar APC

An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC na jihar Abia, Chief Donatus Nwamkpa, yayinda mutan jihar ke sauraron zuwan shugaba Muhammadu Buhari jihar domin yakin neman zabensa karo na biyu.

Kakakin jam'iyyar APC na jihar, Kwamred Benedict Godson, ya tabbatar da haka ga jaridar Daily Trust da safiyar nan.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa kakakin hukumar yan sandan jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, ya ce an tura akalla jami'an yan sanda 1000 domin tabbatar da tsaro yayinda shugaba Buhari zai kawo ziyara jihar.

Mista Ogbonna ya bayyana hakan ne a hira da ya yi tare da jaridar NAN a garin Umuahia ranan Litinin inda yayi bayanin irin shirye-shiryen da sukeyi kan wannan ziyara.

Ya ce za'a hana motoci wucewa a wasu zababbun hanyoyi daga karfe 7 zuwa karfe 2 na rana domin shugaba kasa zai wuce ta wajen.

Yanzu-yanzu: Yayinda ake sauraron zuwan Buhari a Abia, anyi garkuwa da shugaba jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Yayinda ake sauraron zuwan Buhari a Abia, anyi garkuwa da shugaba jam'iyyar APC
Source: UGC

A bangare guda, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira babban filin jirgin saman Sam Mbakwe da ke Owerri, babban birnin jihar Imo inda zai gudanar da yakin neman zabensa karo na biyu.

Shugaba Buhari ya samu kyakkyawa tarba daga wajen jigogin jam'iyyar a filin jirgin saman. Jam'iyyar All Progressives Congress ta garzaya da yakin neman kujeran shugaba kasa yankn kudu maso gabashin Najeriya da aka fi sani da yan yan kabilar Ibo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel