Onnoghen: Sanatocin APC a majalisar dattawa sun kalubalanci Saraki, sun yi adawa da kai Buhari kotu

Onnoghen: Sanatocin APC a majalisar dattawa sun kalubalanci Saraki, sun yi adawa da kai Buhari kotu

- Yan APC a majalisar dattawa sun janye mambobinsu daga wani kara da majalisar ta shigar akan batun dakatar da Walter Onnoghen

- Jiga-jigan jam’iyyar sunce ba su gana don yanke wannan hukunci ba

- Majalisar Dattawan Najeriya dai ta garzaya zuwa kotun kolin kasar domin kalubalantar matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin kasar

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dattawa sun janye mambobinsu daga wani kara da majalisar ta shigar akan batun dakatar da Walter Onnoghen, Shugaban alkalan Najeriya.

A wani jawabi dauke da sa hannun Ahmed Lawan, Shugaban majalisa, a daren ranar Litinin, 28 ga watan Janairu jiga-jigan jam’iyyar sunce ba su gana don yanke wannan hukunci ba.

Onnoghen: Sanatocin APC a majalisar dattawa sun kalubalanci Saraki, sun yi adawa da kai Buhari kotu

Onnoghen: Sanatocin APC a majalisar dattawa sun kalubalanci Saraki, sun yi adawa da kai Buhari kotu
Source: Facebook

Da farko dai a wata sanarwa daga Yusuph Olaniyonu, mai Magana da yawun Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya sanar da cewa majalisar dattawa ta shugar da wani kara kotun koli akan dakatar da Onnoghen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

KU KARANTA KUMA: Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari

Jawabin ya kuma bayyana cewa majalisar dattawan ta janye wani shiri na ganawa da ta so yi a ranar Talata don tattauna lamarin.

Sai dai sabanin haka, jiga-jigan na APC sun nesanta kansu daga wannan matakin.

Jim kadan bayan jiga-jigan na APC sun saki jawabi, sai hadimin Saraki, Olu Onemla yace lallai shugabancin majalisar dattawan sun hadu don yanke wannan hukuncin.

A baya mun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta garzaya zuwa kotun kolin kasar domin kalubalantar matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin kasar Walter Onnoghen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel